Daga USMAN KAROFI
Wasu ma’auratan jinsi ɗaya, William da Zachary Zulock, sun samu hukuncin ɗaurin shekaru 100 babu yiwuwar beli a jihar Georgia, Amurka.
Ma’auratan sun yi laifin yin amfani da ‘ya’yan su maza guda biyu wajen aikata fyaɗe da kuma kirkirar hotunan batsa. Yaran biyu, ‘yan shekaru 12 da 10, an ce sun fito ne daga wata cibiya ta musamman ta Kiristoci da ke kula da marasa lafiya. William ya kasance ma’aikacin gwamnati yayin da Zachary yake aiki a banki.
Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan suna tilasta wa yaran yin ayyukan batsa tare da ɗaukar bidiyo da hotuna don rabawa wasu. Wani lokaci, Zachary ya tura sako a Snapchat yana cewa, “Zai yi lalata da ɗansa a yau da dare,” tare da wasu hotunan batsa.
Bayanan da suka fito daga wata ƙungiyar masu aikata batsa da aka kama sun nuna cewa ma’auratan suna cikin jerin masu ƙirƙirar hotunan batsa tare da yaran su.
Wannan lamari ya kai ga hukuncin ne bayan wani bincike mai zurfi da aka gudanar. A gaban kotu, William da Zachary sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su, ciki har da fyaɗe mai tsanani, lalata yara, da kuma ƙirƙirar batsa. Alƙalin shari’ar, Randy McGinley, ya bayyana wannan lamari a matsayin “mai matuƙar muni” tare da yabawa ƙoƙarin waɗanda suka tabbatar an yi adalci.
McGinley ya kuma jinjinawa jarumtar yaran guda biyu, yana cewa, “munin aikin da ma’auratan suka aikata ba zai taɓa kai ƙarfin jarumtakar da waɗannan yara suka nuna ba.” Wannan hukunci ya zama babban darasi ga masu aikata irin wannan laifi, da kuma ƙara ƙarfafa tsaron yara masu rauni a cikin al’umma.
