‘Yan sandan INTERPOL sun yi shelar neman ‘yan Nijeriya 14 ruwa a jallo

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) ta ayyana wasu ‘yan Nijeriya 14 a matsayin waɗanda ake nema bisa zargin aikata laifuka daban-daban kamar fataucin mutane da miyagun ƙwayoyi, fashi da makami, yaudara, da jabun takardu.

A wata sanarwa da ta fito daga Interpol, sun ce waɗannan mutane suna fuskantar tuhuma a ƙasashe daban-daban kan rawar da suka taka a wasu ayyukan laifi. Sunayen waɗanda ake nema sun haɗa da Felix Omoregie, wanda ake zargin shugabantar wata ƙungiyar laifi a Belgium, wadda ke amfani da ƙananan yara wajen karuwanci da Jessica Edosomwan, wadda ake zargin fataucin mutane a Faransa.

Haka kuma, akwai Uche Egbue wanda ake nema a Argentina kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi, Jude Uzoma a Brazil, da Chinedu Ezeunara a Uruguay, duka suna fuskantar zargin fataucin ƙwayoyi. A Nicaragua, Benedict Okoro yana fuskantar tuhuma kan aikata laifi a cikin ƙungiyar masu laifi, yayin da Bouhari Salif ake nema a China kan safarar miyagun ƙwayoyi.

Sauran sun haɗa da Timloh Nkem, wanda ake nema a Kanada kan zargin cin zarafin mata da kuma karya sharuɗɗan beli. Austine Costa da Okromi Festus suna fuskantar zargi a Indiya kan haɗa kai wajen aikata jabun takardu da yaudara.

Haka kuma, Angola na neman wasu mutum uku kan zargin aikata fashi da makami da garkuwa da mutane, yayin da Denmark da China ke zargin wasu biyu da fataucin mutane.

Interpol ta bayyana cewa sanarwar Red Notice ba izinin kama mutum kai-tsaye bane, sai dai buƙatar taimako daga hukumomin tsaro na duniya don gano wurin da waɗanda ake nema suke, domin ɗaukar matakin doka. Sun kuma yi kira ga duk wanda ke da bayanai kan waɗannan mutane da ya tuntuɓi hukumomin tsaro mafi kusa.

By ukarofi