Shin kasafin Nijeriya na 2025 ya kasaftu?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ka’ida ce kowace shugaban ƙasa ya gabatar da kasafin kuɗi ga haɗin guiwar Majalisar Dattawa da wakilai inda hakan kan ya zama bigiren da za a duba domin tsara kasafin ta hanyar ragewa ko ƙara yawa bisa yanda ‘yan majalisa su ka ga ya dace da sassan gwamnati da kasa baki ɗaya. Ba wani abun mamaki yadda kasafin ɓangaren tsaro ya kan kwashi kaso mafi tsoka don yadda sassan Nijeriya ke fama da matsalar. Kama daga kudu maso gabar inda har yanzu a ke fama da ’yan waren Biyafara masu son ɓagarewa daga Nujeriya zuwa arewa maso yamma da ke fama da ɓarayin daji har ma yanzu ga Lakurawa da su ka shigo daga ƙetare su ka haɗa kai da wasu ‘yan ƙasa. Can ma arewa maso gabar har yanzu ba a gama da ‘yan Boko Haram ba. Wato ma’ana dai a nan idan sashen tsaro ya buƙaci kasafi mai yawa ba za a yi tababar miƙa ma sa ba; amma hakan ba ya na nuna za a iya gamaa da matsalar ba ne. Abun ma tambaya yaya a ke kashe kuɗi a wannan sashe? Yaushe kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu? Shin kuɗi ne kaɗai a ke buƙata wajen samar da tsaro?

Ga dai tambayoyi daban-daban da ke son amsoshi masu gamsarwa. Bangaren tattalin arziki da ya zama cikin ƙunci inda akasarun talakawa ba sa iya samun abinci sau uku a wuni don zare tallafi musamman kan man fetur. Kazalika zai yi wuya gwamnati ta iya biyan mafi ƙarancin albashin da zai iya ragewa ma’aikata ɗawaniyar su a tsawon wata. Hanyoyin samun kuɗin da za a dau nauyin kasafin daga man ɗanyen man fetur da a ke sayarwa, harajin fiton kaya da hanyoyin tara harajin cikin gida da sauran ɓangarorin da kan samar da kuɗin shiga. Duk waɗannan hanyoyin a zahiri ba sa wadatar da gwamnati samun kuɗin da za ta iya ɗaukar nauyin kasafin nan sai an ciyo bashi daga ƙetare.

Haƙiƙa Nijeriya na ƙara afkawa cikin jibgin bashi da Hausawa ke cewa hanji ne ya na cikin kowa. Hatta cikin watan nan shugaba Tinubu ya mikawa majalisa buƙatar ciwo bashi don ɗaukar nauyin kasafin kuɗi na 2024. Gaskiya ba daga kan shugaba Tinubu a ka fara ciwo bashi ba amma batun shi ne yaushe wannan bashin zai ragu ko ma a ce za a iya gudanar da harkar kasafi ba tare da bashin ba?. Masana sun sha bayyana hanyoyin da za a iya nasara kan wannan amma da alamu wasu hanyoyin da ke sa kudin gwamnati na zurarewa haryanzu ba a cimma nasarar toshe su ba. Ga sauran ɓangarori masu bukatar kuɗi da su ka haɗa da sashen ilimi, lafiya, aikin noma, shunfuɗa hanyoyi da sauran su. Za a dai gabatar da kasafi da bayanai da a ke son gamsar da jama’a komai zai tafi daidai. Inda gizo ke sakar shi ne jami’an gwamnati da a kan warewa ma’aikatun su kasafin nan in sun samu kason su ta yaya su ke sarrafa shi?

Neman izini daga majalisar dokoki na ciwo bashin dala biliyan 2.209 da shugaba Tinubu ya yi na haddasa muhawara.

Shugaba Tinubu ya tura buƙatar don ɗaukar nauyin gibin kasafin kuɗin bana da ma zai kare aiki a watan nan.

Tun zamanin mulkin shugaba Buhari a ka daidaita kasafin kudi ya fara daga watan Janairu ya kare a watan Disamba.

Ofishin kula da bashi na Nijeriya DMO ya bayyana cewa jibgin bashin da ke kan Nijeriya ya tashi daga Naira tiriliyan 97.34 a Disambar bara zuwa Naira tiriliyan 121.67 a watan Maris da hakan ya auku musammana saboda sauyawar canjin kuɗi.

Mutane a kafafen labaru na nuna damuwa kan tarin bashin da su ke ganin ba a ganin amfanin sa a zahiri.

Masana na nuna damuwa kan yadda jibgin bashi ya yiwa Nijeriya kawanya kuma gwamnati ba ta daina hankoron neman sabon bashi ba.

A taron Zauren ɓOA na Muryar Amurka a Abuja masanan sun ce ba laifi ba ne ciwo bashi amma a tabbatar da an yi amfani da shi don inganta rayuwar jama’a.

Masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya ce hatta asalin layin dogo na Najeriya da bashi a ka shunfuda shi don haka ya na da kyau a riƙa gani a kasa ga duk bashin da a ka ciwo.

ɗan Malikin Kebbi Alhaji Musa Abubakar ya danganta matsalar da a ke samu wajen rashin ganin tasirin bashi kan cin hanci da rashawa inda wasu jami’ai kan wawure kuɗin baitul-mali.

Mahalarta taron sun buƙaci masu jan ragamar kasa su sani jama’a na kallon su kuma in sun aikata da kyau za su ga da kyau hakanan ma akasin hakan.

Gabannin gabatar da kasafin kuɗin, majalisar zartarwa ta Nijeriya ta yi zama inda ta amince da kasafin kuɗin shekara mai shigowa ta 2025 da ya kai Naira tiriliyan 47.9.

Ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu ya baiyana amincewar bayan kammala taron majalisar a fadar Aso Rock.

An dora kasafin kan farashin gangar mai dala 75 da kuma canjin Naira a kan dala Naira 1,400. Kazalika da hako gangar mai fiye da miliyan 2 a duk wuni.

Yanzu dai shugaba Tinubu ya shiga majalisar dokoki inda ya gabatar da kasafin bayan jinkirin hakan a asalin ranar da a ka ambata ko a ka yi tsammani a farko.

Da alamun a wannan karo ba a samu zargin gabatar da bayanan kasafin ba tare da mika kundin ba. In za a tuna a bara an samu zargin gabatar da kasafin da kawo akwatunan kundaye da a ka girke gaban majalisa ba tare da ko takarda daya ba. Shugaba Tinubu na cin gajiyar samun majalisa da ke tafiya da shi ba tada jijiyar wuya. In an lura shugaban wanda ko ma dai yaya ya fahimci logar siyasar Nijeriya ya yi tsayin daka ko nasara wajen tabbatar da ‘yan takarar sa ne su ka samu jagorancin majalisar wato Godwill Akpabio a majalisar dattawa da Tajudeen Abbas a majalisar wakilai. Kuma mun san cewa shugabannin majalisa na da tasiri wajen matakan da majalisa ke ɗauka wajen alaƙa da sashen zartarwa. Mun tuna yadda wani kuskure ya sa a majalisa ta 8 shugaba Buhari bai samu jama’ar sa sun jagoranci majalisa ba da hakan ya sa bai yi aiki da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara lami lafiya ba.

Baya ga samar da tsaro akwai matuƙar muhimmancin dakile duk hanyoyin cin hanci da rashawa a Nijeriya. A kwanan nan hukumar EFCC ta bayyana gano rukunin gidaje 756 da ta samu hurumin kwacewa daga kotu da ya zama mafi girman gidaje masu yawa a lokaci ɗaya da hukumar ta samu nasarar bankadowa da karɓewa. Gidajen da ke anguwar Lokogoma a Abuja kamar yanda hukumar ta baiyana mallakar wani tsohon babban jami’in gwamnati ne. Duk da EFCC ba ta bayyana sunan jami’in ba, mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara wato Omoyele Sowore ya ce mutumin shi ne tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele.

Hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta ce ta kwato kimanin Naira biliyan 40 daga barayin biro a tsakanin jami’an gwamnati cikin shekarar nan ta 2024 mai karewa.

Shugaban IICPC Dokta Musa Adamu Aliyu ya bayyana haka a taron bitar aiyukan hukumar na shekara da ya samu halartar shugaban EFCC da sauran jagororin hukumomin da su ka shafi mu’amala da kuɗi.

Dr.Musa Adamu ya ce binciken da su ka gudanar ya bankaɗo aiyukan rashawa masu ban mamaki daga ɓagarorin da ba a ma tsammani.

Cikin misalan da ya bayar har da karbar makudan kudi wajen biyan ma’aikatan bogi da wasu hanyoyin karkatar da kuɗin gwamnati.

Shugaban hukumar EFCC Ola Olukoyede ya karfafa muhimmancin aiki tare tsakanin hukumomin biyu na yaƙi da rashawa na Nijeriya “duk aikin da ya shafi ICPC kar a kai wa EFCC hakanan duk aikin da ya shafi EFCC kar a kawo ICPC,” Inji Olukoyede.

Shi kuma kwamishinan yaƙi da cin hanci na Saliyo da ya zama babban bako  mai jawabi ya koka kan yanda ya ce a kan gudanar da bincike mai kyau amma a kotuna sai a samu cikas wajen wa imma yanke hukunci marar tsauri ko ma masu laifi su zama an wanke su.

ɗaya daga mahalarta taron Dokta Sule Yau Sule ya ce matukar an yaki cin hanci to duk ‘yan kasa za su amfana da arzikin kasa.

Taron ya ƙarfafa cewa kudaden da a ke sacewa sun kai matsayin da za su iya samar da ababen more rayuwa ga dukkan ‘yan kasa.

Kammalawa;

Ba a ɗebe tsammani daga rahamar Allah. A nan ba za mu ce sam Nijeriya ba za ta gyaru ba. Duk da haka gyaruwar na kan kowa daga gwamnati zuwa talakawa. Kowa sai ya ba da ta sa gudunmawar amma na gwamnati shi ne kaso mai tsoka don daga Liman sallah kan ɓaci. Duk hanyoyin da ‘yan kasa za su samu rangwame don aƙalla su riƙa samun abinci ya dace gwamnati ta maida hankali a kai. Idan abinci na da rahusar samu sauran abubuwa za su yi sauƙi. Kaulin nan na cewa “mayunwaci na zama fusatacce” kuma daga fusata a kan samu tsana ga masu riƙe da madafun iko inda ko sun yi abun alheri ba za a gani ba.

By ukarofi