Matsalolin haƙora da yadda za a magance su 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Ciwon haƙora na ɗaya daga cikin curuta mafi ɗaukar hankalin mai tare da su, kuma ciwon ya zama ruwan dare a tsakanin mutane, wataƙila hakan ba ya rasa alaƙa da rashin sanin hanyoyin da ke iya haddasa matsala a haƙoran namu na daga hanyoyin kula da su.

Akwai ɗabi’u da dama da muka maida ba komai ba, amma sukan zama silar kamuwa da wata nau’in cutar haƙora. Darasin namu na wannan sati zai karkata ne kan matsalolin da kuma yadda za a iya magance su, don haka ba za mu samu damar nutsewa cikin bayanin yadda muke cin karo da matsalolin haƙoran da ɗabi’un da ke zama silar samuwar su ba. Wannan darasi ne mai zaman kansa da muke fatan kawo wa masu karatu shi nan da bada jimawa ba.

Matsalolin haƙora suna da yawa, kuma hanyoyin maganinsu ma haka, don haka za mu yi amfani da ɗaya daga cikin ni’imar da Allah Ya yi mana ta ɓangaren tsiro, wato tumfafiya. 

Idan ki na cikin masu fama da matsalar haƙora mai sa matsanancin ciwo na haƙoran, to ki nemi itacen ita wannan itaciya a dafa tare da ɗan gishiri, jar kanwa da kuma ɗan kanunfari. Idan ya ɗan huce, (kada a bari ya huce gabaɗaya, hucewa yadda baki zai iya amsar sa ba tare da ya ƙone ba). Za a dinga cika baki da shi, tsayin mintuna uku, sannan a zubar. Ana maimaita hakan safe da dare.

Haka ma ta ɓangaren mai fama da matsalar Kogon haƙora, idan har mai karatu masani je kan itaciyyar ta tumfafiya, ya san akwai kaɗa cikin ƙwallon tumfafiya, sannan ana samun wani ruwa mai kalar madara yayin da aka cire ƙwallon. Waɗannan ababe biyu ne muke buƙata yayin samar da wannan maganin. Za a ɗauki kaɗar ne, a dangwali ita wannan madarar, sai a sanya a daidai inda kogon yake. Za a aikata hakan sau ɗaya a rana. In sha Allahu za a wayi gari an magance wannan matsala.

Idan mun koma kan matsalar tsutsar haƙori, ita ma za a iya amfani da tumfafiya don samun sauƙi daga matsalar. Ta yaya? Za a tafasa saiwar tumfafiya a kuskure baki da ruwan suna masu ɗumi, safe da dare, tsayin kwanaki uku.

A wasu lokuta kana iya samun kanka a jerin masu matsalar fitar jini daga haƙoranka, ya Allah ta sanadiyyar motsa haƙoran da yawa, kamar ƙaramin duka a baki, ko ƙoƙarin cire wani abu da ya maƙale a tsakanin haƙora, kamar nama. Duk da cewa, sau da yawa kogon haƙora na tsakanin haƙori da haƙori kan iya haifar da zubar jini, a sa’ilin da wani abinci ya samu gurbin zama a wurin, lokuta da dama idan ka yi yunƙurin cire shi ko bayan ka cire shi, jini kan biyo baya, wani sa’in har da ciwo. Baya ga wannan matsala, akwai ta rashin tsaftace baki yadda ya kamata, wannan kuwa magance ta na tasiri ne bayan an yawaita tsaftace haƙoran. Sai kuma akwai cutar haƙori mai zaman kanta ta zubar da jini lokaci-lokaci, wani sa’in ma ba2ani dalili daga cikin dalilan da aka jero a sama. A wannan gaɓa muna magana ne kan ita wannan cuta mai haifar da zubar jini a baki. Idan kuna tare da ita, sai ku samu ganyen tumfafiya tare da sassaƙen ta, kanunfari kaɗan da kuma ɗan gishiri. Za a dafa cikin ruwa mai tsafa, sai a dinga kuskura baki da ruwan a lokacin da zafin su ya yi daidai da yadda ba ki zai iya amsa. Ana aikata hakan safe da kuma dare Idan za a kwanta.

A wasu lokuta rashin hasken haƙora kan zama matsala ga mai tare da shi, saboda sau da yawa idan aka kalli haƙoran sai a yi wa mai su kallon ƙazami, duk da cewa, yana wanke su yadda ya kamata. Sau da yawa akan bazama neman man wanke baki da ya dace da haƙoran, a namu tunanin rashin dace da man baki na ƙwarai ne ya janyo hakan. Sai dai abinda ba mu sani ba, wannan matsala ce da ke buƙatar a magance ta kamar kowacce, kafin a ga haƙoran a yanayin da ake buƙata. Kuma za a iya amfani da busashen furen tumfafiya tare da alif (kaɗan sosai), sai a yi amfani da asuwaki, ana dangwalawa, ana gurje haƙoran sosai da shi. Sannan an bada minti ɗaya zuwa uku kafin a wanke bakin, amma ba tare da an haɗe wani abu daga cikin haɗin ba.

A ɓangare ɗaya, akwai disashewar haƙora da ke samuwa ta sandin yawan cin goro, ko shan taba sigari ko ta gari. Waɗannan kan kai haƙora ga tabo baƙi da ka ɓata haskensu. Wannan matsala na da bambanci da wadda muka yi magana kanta a sama. Ita wannan za a fara da tsagaitawa ko daina amfani da abinda ke haddasa matsalar kafin a nemi lemun tsami a haɗa da furen tumfafiya a dafa sosai, sai a dinga kuskure bakin da su idan sun ɗan rage zafi, sai a bi baya da buroshi a darje haƙoran.

By ukarofi