Gwamna Abba ya halarci jana’izar mahaifiyar gwamnan Jigawa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Jigawa

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya halarci Sallar jana’izar mahaifiyyar gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi(Dan Moɗi)

Gwamnan Kanon wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin masu ruwa da tsaki zuwa ƙaramar hukumar Kafin Hausa dake Jihar Jigawa yayin rufe marigayiyar Hajiya Maryam Namadi Umar.

Yayin halartar sallar jana’idar gwamnan yayi addu’ar samun rahama da kwanciyar kabari cikin lumana ga mahaifiyar gwamnan na Jigawa.

‘Wannan babban rashin ba na gwamna Umar Namadi bane kaɗai, kafatanin al’ummar arewa ne da ƙasa baki ɗaya.

Wakilin mu ya ruwaito cewa Hajiya Maryam Namadi ta rasu ne a anguwar Gamabawa da ke ƙaramar hukumar Kafin Hausa bayan tayi fama da gajeruwar rashin lafiya,an kuma yi jana’izar ta kamar yadda addinin musulnci ya tanadar.

Haka zalika wasu daga cikin makusantan ta sun shaida cewa marigayiya Maryam Namadi ta rasu tana da shekaru sama da 80 a duniya,inda ta bar ya’ya da jikoki da dama.

Cikin waɗanda suka samu halartar sallar jana’izar sun haɗa da mataimakin gwamnan na Jigawa Injiniya Aminu Umar da wasu sarakunan dake jihar ta Jigawa kama daga sarkin Dutse, Sarkin Haɗeja da sauran al’umma na ciki dana wajen Ƙasar nan.

By ukarofi