Badaƙalar Dala 35m: Kotu ta tusa ƙeyar daraktan matata zuwa Kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC ta gurfanar da Darakta-Manaja na matatar Kamfanin ‘International Refinery and Petrochemical Limited’, Akindele Akintoye bisa zargin sa da hannu a badaƙalar Dala miliyan 35.

A ranar 31 ga watan Oktoba, 2024 ne EFCC ta kama Mista Akintoye inda ta tsare a ofishinta dake Abuja.

Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ne yake hukunci game da shari’ar.

Wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafin X, ya ce ana zargin Akintoye ne da karɓar kuɗaɗen daga Hukumar Ci-gaban Ayyuka da kula da su ta Ƙasa da sunan zai gina matatar da za ta riƙa fitar da mai ganga 2,000 a kullum da samar da maɗaukan jiragen ruwa da rijiyar gas da sauran su a yankin ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.

Bayan yunƙurin neman belin wanda ake tuhuma da laifin ne, sai Alƙali Nwite ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2024 don yanke hukunci.

Daga nan ne ya umarci a tsare Akintoye a gidan yarin Kuje dake babban birnin zuwa lokacin da za a sake zama a kotun game da batun.

By Babaji