Yan sanda a Katsina sun ceto mutane 10 a hannun ‘yan bindiga.

Spread the love

‘

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan sanda a Katsina sun sami nasarar ceto fasinjoji 10 da ‘yan bindiga sukai ƙoƙarin sacewa a ƙaramar hukumar Jibiya.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata hira da manema labarai.

Ya ce, lamarin ya faru ne a Magama Jibiya inda ‘yan bindiga ɗauke da manyan bindiga ƙirar AK 47 suka kaiwa wata motar haya ɗauke da fasinjoji 10 farmaki.

Da samun labarin lamarin ‘yan sanda suka garzaya wajan inda akai ta bata kashi da ‘yan ta’addan.

ASP Sadiq ya bayyana cewa cikin fasinjan mutum biyu sun mutu sakamakon munanan raunuka da suka samu, mutum huɗu na asibiti ana masu magani bayan raunuka da suka samu.

Yace yanzu haka ‘yan sanda sun shiga daji domin farautar waɗannan ‘yan bindiga.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba wa ‘yan sandan da suka kuɓutar da mutanen tare da kira ga alumma da su rinƙa ba jami’an tsaro bayanan sirri na maɓoyan waɗannan miyagun mutane.

By ukarofi