An yi wa fiye da mutane 100 aikin ƙaba da ƙari kyauta a Kano

Spread the love

Sama da yara 100 ne suka rabauta da aikin ƙaba da ƙari kyauta a Karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano.

A sanarwar da Jami’ar Yada Labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Kansilan Lafiya na yankin, Malam Bashir Shu’aibu, ya ce, sama da mutum dari ne suka amfana da aikin kaba da kari kyauta, a cigaban ayyukan inganta lafiyar al’uma, wanda Gwamnatin Jihar Kano da Karamar Hukumar Bichi ke daukar nauyi.

Malam Bashir Shu’aibu ya bayyana cewa aikin yana gudana ne a asibitin Kula da Lafiya a Matakin Farko dake Mazabar Saye, inda ya yi fatan alheri ga Gwamnatin jiha da Majalisar karamar hukumar, bisa wannan aikin alheri tare da kuma addu’ar samun lafiya ga dukkan majinyatan da suka rabauta da wannan aiki.

A hannu guda kuma, yara mata ‘yan kimanin shekaru tara 9 su dari tara da da hamsin da uku 953 ne, aka yi wa Allurar Rigakafin Kansar Mahaifa a karamar hukumar, inda aka samu damar yi wa yara dari biyar da hamsin da tara 559, a makarantun firamare da kuma yara dari uku da casa’in da hudu 394, a cikin gidaje dake unguwanninsu.

Shugaban Sashen Kula da Lafiya na yankin, Malam Kabiru Abubakar Gwarzo, ya jinjina wa Gwamnatin Kano bisa dimbun ayyukan taimakon al’umma da tasa a gaba, musamman bangarorin ilimi da lafiya. Haka zalika, ya yaba wa masu rike da sarautu tare da jan hankalin al’uma.

“Shugaban karamar hukuma, Alhaji Hamza Sule Mai fata ya ba da gudunmawa sosai game da aikin masu larurar kaba, haka bangaren Allurar Rigakafin Kansar Mahaifa ta yara, muna jawo hankalin iyayen yara su dinga kawo ‘ya’yansu ana yi musu domin rigakafin wannan kansar mahaifa dake addabar yaranmu. Sannan muna godiya bisa hadin kai da masu rije da sarautu suke ba mu game da wannan aiki”, inji shi.

By Babaji