
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Bola Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyuka da Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya samar a Maiduguri, Babban Birnin jihar.
Shugaban ƙasar ya buɗe manyan makarantu uku, wato ‘mega schools’ da kuma motocin lantarki da babura masu ƙafa uku, wato adaidaita guda 620, waɗanda gwamnan ya samar.
An yi taron ƙaddamarwar ne a wurare mabambanta, inda Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamna Zulum bisa jagoranci na gari da yake ƙoƙarin aiwatar wa al’ummar jiharsa.
Tinubu ya ce: “Ina taya Gwamna da al’ummar Jihar Borno murna bisa wannan gagarumin sauyi. Gwamnati dai game da jama’a take, kuma Farfesa Zulum yana yin aiki mai kyau wajen kula da al’umma.”
Shugaban ƙasar ya bayyana ayyukan da aka ƙaddamar a matsayin hujja ta ingantacciyar shugabanci da kuma tsarin cigaba mai ɗorewa ga jihar.
Makarantun da aka ƙaddamar sun haɗa da, Mafoni Day Secondary School, Bola Ahmed Tinubu Government Day Secondary School da kuma Mafoni Primary School.
Wadannan makarantu suna cikin Shirin Gagarumar Makarantu 104 (104 Mega Schools Initiative) na Gwamna Zulum, wanda aka ƙirƙira domin inganta samun ilimi mai inganci da kuma farfaɗo da fannin ilimi bayan fiye da shekaru goma na rikicin Boko Haram da ya addabi jihar da kewayenta.
Kowace makaranta na ɗauke da azuzuwa na zamani, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu, wuraren motsa jiki da ofishin gudanarwa, domin samar da ingantaccen yanayin koyo.
Kazalika, Tinubu ya ƙaddamar da tashar jirgin sama ta kasa da ƙasa a Filin Jiragen Sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri, domin shirin fara zirga-zirgar jiragen sama na matakin ƙasa-da-ƙasa.
Da yake jawabin, Gwamna Zulum ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa goyon bayan da take ba wa jihar, tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na sake gina ababen more rayuwa, tattalin arziƙi da jarin bil’adama na Jihar Borno.
Taron ya samu halartar jami’an tarayya da na jiha, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma.
Shugaba Tinubu ya kammala ziyararsa ta jihar Borno ne da halartar bikin auren ɗan tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, wanda aka gudanar a Babban Masallacin Maiduguri.


