
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kociyan Brazil, Carlo Ancelotti, ya ɗora laifin cire ƙasar da aka yi a gasar Kofin Duniya na 2026 a zagayen ‘yan 16 akansa, yana mai cewa an samu ƙwacewar lissafi ne a yayin da aka je hutun shan ruwa a wasan da ta kara da Norway.
Daɗaɗɗen kocin ya amince cewa matakin da ya ɗauka wajen sauya salon wasan ne ya sanya Erling Haaland ya zura ƙwallon da ya ba Norway nasara akan Brazil, kamar yadda ya bayyana a wata hira da da ESPN ta wallafa.
Ya bayyana cewa, Brazil ta kasance mai jan ragamar wasan har zuwa dab da tashi a wasan, duk da cewa su ma ‘yan Norway sun riƙe ƙwallo a yankinsu na filin wasan.
Ancelotti ya ƙara da cewa, ya yi kuskuren karantar halin wasan ne bayan hutun shan ruwan, lamarin da ya sanya shi yin wasu sauye-sauyen da ba su dace ba da yanayin wasan.
Gabanin tafiya hutun rabin lokaci ne kocin ya gabatar da Neymar da Danilo Santos bayan cire Gabriel Martinelli da Rayan.
Duk da cewa, kocin ya kare ƙoƙarin Neymar, ya kuma tabbatar da gazawarsa wajen sauya baki ɗaya tsarin ‘yan wasan baya da na tsakiya domin sanya ‘yan benci.
