Annobar kwalara ta jefa Jihar Jigawa cikin alhini da zulumi bayan mutuwar mutum 41

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata annobar cutar amai da gudawa, wacce ake kyautata zaton cutar kwalara ce, ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 41 a Jihar Jigawa, inda mata da ƙananan yara suka fi kamuwa da cutar. ɓarkewar cutar da ta shafi al’ummomi da dama, ta sa jihar cikin alhini da zulumi.

ƙauyen Gatafa da ke ƙaramar hukumar Auyo na daga cikin waɗanda lamarin ya fi shafa, inda aka ƙirga sabbin kaburbura guda 41 da wakilin gidan talabijin na Channels, Sadiƙ Iliyasu, ya yi a maƙabartar ƙauyen.

Sauran al’ummomin da cutar ta ɓullawa a garin Auyo sun haɗa da Auyakayi, Gatafa, Muran, Tsidir, Shawara, Tsaka, Majiya, Ayama, Anauya, da Kalgwai, waɗanda dukkansu sun yi rahoton mutuwar mutane tare da saurin yaɗuwar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Jigawa, Dr. Muhammad Kainuwa, ya tabbatar da ɓullar cutar tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa domin shawo kan cutar.

“Muna sane da lamarin kuma mun tura ma’aikatan lafiya da kayan aiki zuwa yankunan da abin ya shafa. Ana kuma ɗaukar matakan hana afkuwar asarar rayuka,” inji shi.

Domin inganta harkar kiwon lafiya da magance ƙarancin ma’aikatan lafiya, Kainuwa ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da jihar ke yi.

“A halin yanzu gwamnatin jihar tana gina gidajen ma’aikatan jinya a cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 60 domin inganta jin dadin ma’aikatan kiwon lafiya a yankunan karkara.

Bugu da ƙari, muna aiki don haɗa mutane kusan 500,000 masu rauni a cikin tsarin inshorar lafiya na jihar don samar da ingantacciyar hanyar samun lafiya,” inji shi.

Haka kuma, a ƙoƙarin da ake na ɗinke barakar da ake samu a ɓangaren ma’aikata, gwamnati ta ɗauki nauyin karatun likitanci zuwa kasashen waje.

“Wannan wani ɓangare ne na dabarun mu na dogon lokaci don magance ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya da kuma tabbatar da cewa muna da bututun ƙwararru,” inji Kainuwa.

Gatafa mai tazarar kilomita shida daga hedikwatar karamar hukumar Auyo, rahotanni sun ce an samu asarar rayuka masu yawa sakamakon rashin tsafta da kuma rashin tsaftataccen ruwan sha.

Ahmadu Adamu, wani mazaunin Gatafa da ya rasa ‘yan uwa uku ciki har da matarsa, ya ce, “Cutar ta yadu cikin sauri, kuma ba mu da hanyar da za mu iya dakile ta. Na rasa matata, da wasu ’yan uwa biyu. Ya yi ɓarna.”

Wani mai tsira da rai Muhammad Chiroma ya ruwaito cewa sama da mutane 200 ne lamarin ya shafa a Gatafa. “Cutar ta same mu sosai. Mutane da yawa sun mutu, wasu kuma suna ci gaba da fafutukar ganin an ceto rayuwarsu,” in ji Chiroma.

Yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da mayar da martani kan rikicin, ƙungiyar likitocin Nijeriya NMA ta nuna matuƙar damuwa kan matsalar ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Jigawa, lamarin da ya dagula ƙoƙarin shawo kan cutar.

By ukarofi