Anya Nijeriya za ta gyaru kuwa? 

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Bar batun gwamnati, mu ma mutanen da ake mulka muna da tamu irin matsalolin da ba su da iyaka. Akwai wata rana na hau Adaidaita Sahu (Keke Napep) daga titin Zoo Road ne zuwa Bata. Tun da akai ƙarin mai kowa ya san Naira 300 ne kuɗin, amma na miƙa wa Mai Napep kuɗi zai ba ni canji ya juya yana shirin tafiya wai ya gan ni Alhaji. Na ce, Alhaji bai san zafin nema ba? Me ya sa na hau Napep ɗinka na bar tawa motar? Ba ni canjina na wuce ko ka ɗauka yau na shigo Kanon daga Zariya?

Siyan abu kuwa wani lokacin haushi nake ji shi ya sa na fi son na je ‘super market’ na siya saboda su ga kuɗin nan a rubuce, idan ya yi maka ka siya ka biya, idan bai yi maka ba ka ƙara gaba ba matsala. Amma idan akan hanya za ka siyi abu yadda suka gan ka haka za su ƙimanta maka, idan suna siyar da abun Naira 200 idan sun gan ka da jiki luwai-luwai za su iya ce maka Naira 2000. 

Kada ma masu gyara su ji labari. Na taɓa kai gyaran motata aka ce min Naira 150,000. Na dawo da ita na ajiye, Ina ta addu’a Allah ya kawo min sauƙi. Sai ga wani ya zo ya gyara min a Naira 28,000. 

Jiya-jiyan nan ba wani nisan duniya ‘balance’ min gyaran mota Naira 40,000. Na lallaɓa shi ɓin da ya faɗa min haka na ba shi Naira 20,000, kuma gyaran daga baya wani ya faɗa min ba zai wuce Naira 10,000 ba duk tsadarsa. Na ce ya je ya ci zakkarsa ta wannan shekarar.

Yanzu haka Ina son siyo kayan Chana, amma RMB sun ƙara shi kuma babu ruwan gwamnati son zuciya ne kawai irin na masu canji, don sun ga ana yin canjin sosai. Ina tayawa aka ce min Naira 207. Kafin na saka kuɗi sai aka ce min ya koma Naira 211. Kafin na buɗe baki na yi magana har ya koma Naira 218.9 . Ji Wani hauka! Ba fa gwamnati ba ce ta yi wannan ƙarin, kuma da su waɗannan mutanen za mu haɗu mu zagi gwamnati. 

Tabbas ’yan Nijeriya ko na ce baƙaƙen fata ba sa bambance haram da halal. Su kawai sun ɗauka naman alade ko naman kare shine haram ko ka sha giya. Amma wajen neman abincinsu ba su da wannan ganewar da bambancin. Hatta masu dako ana samun irin haka cikin lamarinsu idan suka ɗaukar wa Alhaji kaya wajen da bai fi a ba su Naira 1000 ba, sai su kira maka Naira 5000. 

Ba iya waɗanda na bayar da misali ba ne kaɗai ke da matsala kusan kowa da kowa ne har ni ma mai rubutun nan, Uncle Larabi, Ina da irin tawa matsalar. A ɓangaren gwamnati da yawan ma’aikatan gwamnati kusan kaso 95% ba su gane cewa, albashin da ake biyan su shine kuɗin aikin da suke yi ba.

Idan ƙara ka kai ‘police station’ kuɗinka ne zai yi kuka sai ka ga gwara ma ka haƙura idan ba haka ba za ka kashe kwatankwacin kuɗin da aka cuce ka, ƙarshe sai ka ga ma ba amfani karɓar wancan kuɗin, ba wanda zai yi maka aiki kyauta ya gane cewar, aiki yake wa gwamnati da ƙasarsa, a’a, tuni wannan batun ya wuce.

Hatta a bankuna da asibitoci da sauran guraren aikin gwamnati idan ka je ka ga ana haba-haba da kai ‘Alhaji sannu da zuwa. Me za ai maka?’ To, aljihunka ne zai kuka. Idan ba ka bayar ba a ji haushin ka ko a zage ka. Gobe da an gan ka sai a ɗaure maka fuska ko a yi maka wata ƙaryar. 

A Wannan rubutun ba wai Ina yi don na kare gwamnati ba ne, a’a, na yi ne don jan hankali gare mu da mu gyara zukatanmu da halayenmu. Babu wanda don ya bar kuɗin gado za a rubuta masa lada. Babu wanda dan ya mutu ba ko sisi za a ba shi zunubi. Amma ka sani idan ka ciyar da iyalanka da haram za a ba ka zunubi. Kai kanka idan ka ci haram za ka samu zunubi. Idan ka tara dukiyar haram ka bar wa yaranka sun ci halal kai kuma zunubin zai ta bibiyar ka har zuwa ranar sakamako (The day of Judgement), wanda sanda muke yara muke kira da (No Fashality). Ba fasha. Duk abin da ka gani kai ne ka aikata na alheri ko sharri. 

Don Allah ’yan uwa mu kiyaye da ’yar wannan nasiha da na muku. Mu yi ƙoƙarin gyara zukatanmu da ayyukanmu na zahiri da baɗini. Duniya ba matabbata ba ce. Lahira ita ce tabbas! Don haka a duniya ake haɗa ‘balance’ na guzurin tafiya lahira. 

Dan uwanku, ƙaninku, abokinku, Uncle Larabi, wanda za a iya samun sa a 08065418892.

Juma’a, 12 ga Disamba, 2025

By ukarofi