APC ta dakatar da tsohon gwamnan Ogun Gbenga Daniel kan zarge-zargen cin hanci da rashawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), reshen jihar Ogun, ta dakatar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel.

An dakatar da tsohon gwamnan ne tare da ɗaya daga cikin masu yi masa biyayya, Kunle Folarin bisa zargin rashin ɗa’a ga jam’iyyar.

Nuberu Olufemi, mai magana da yawun jam’iyyar APC a Ogun, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (SWC) ya amince da dakatar da Daniel da Folarin a ranar Talata.

Olufemi ya ce an kafa kwamitin ladabtarwa a gunduma ta 4 a ƙaramar hukumar Shagamu kan “ɗa’a da ake zargin tsohon gwamnan Ogun da aikatawa a kan dokokin jam’iyya.

Kakakin Jam’iyyar APC na Ogun ya ce an gayyaci Daniel da ya gurfana gaban kwamitin domin kare zargin amma ya kasa yin hakan.

Ya ƙara da cewa Folarin ya kuma gaza gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa da jam’iyyar APC ward 6 ta kafa a ƙaramar hukumar Shagamu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Sun rubuta wa mambobin da ake bincike, suna gayyatar su zuwa taron ladabtarwa da za a saurare su, sannan a ba su damar gabatar da hujjojin kare su ko neman afuwa daga jam’iyyar,” inji sanarwar.

“Duk da haka, dukkan mambobin biyu sun kasa amsa gayyatar da aka yi musu a rubuce, sun kasa bayar da kariya a rubuce, sun kuma kasa halartar tarurrukan ladabtarwa da za a ba su damar kare kansu.

“Saboda rashin zuwan su da gangan da kuma rashin bayani, kwamitocin sun tattauna kamar yadda aka tsara, sun ji ta bakin shaidun da suke da su, sun yi la’akari da hujjojin da ake da su, kuma sun tattauna kan zargin.

“Baya ga abubuwan da ke sama, kwamitocin sun samu sanarwar cewa mambobin da ake bincike sun rika cin zarafin ‘ya’yan jam’iyyar tare da gargadin mambobin jam’iyyar kan ba da haɗin kai ga kwamitocin.

“Mambobin da ake binciken sun kasance suna amfani da matsayinsu a cikin jam’iyyar wajen tursasa mambobin jam’iyyar su janye karar da aka shigar musu.

By ukarofi