
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC a Jihar Edo ta yi kira ga tsohon shugabanta na ƙasa, John Odigie Oyegun da ya biya bashin Naira miliyan 150 da ake zargin sa da riƙe wa jam’iyyar.
APC ta ce an tara bashin ne a lokacin d Odigie Oyegun yake mamba kuma shugaban jam’iyyar ciki har da kasancewarsa shugabanta na farko.
A wata sanarwa daga shugaban jam’iyyar na jihar, Emperor Jarrett Tenebe, APC ta yi ikirarin cewa Oyegun ya ƙi amsa buƙatun biyan wasu kuɗaɗe, wanda hakan ya sa adadin bashin ya kai miliyan N150.
A cewarsa, basusuka sun taru ne daga kuɗaɗen aro da aka ciyo a ƙarƙashin jagorancin Oyegun a APC da kuma kuɗaɗe zama mamba da ya gaza bayarwa a tsawon wa’adin zamansa acikin jam’iyyar.
Da yake tsokaci akan al’amarin, Oyegun ya yi watsi da ikirarin, inda ya bayyana su a matsayin abin da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma da kuma ake ƙoƙarin siyasantarwa.
Ya ce, wannan al’amari zai sa “jama’a su yi dariya akan haka”, yana mai bayyana cewa samuwar ADC ta sanya su acikin matsalolin fargaba.
Ya ƙara da cewa, APC ta mayar da hankali akan yi wa al’umma hidima, ta gwammace ta yi ƙoƙarin tayar da hatsaniya da rikici acikin ‘yan ɓangaren adawa.
