Donald Trump ya yabi Remi Tinubu a taron addu’ar ƙasa na Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yaba wa Uwargidan Shugaba Bola Tinubu, wato Sanata Oluremi Tinubu, inda ya bayyana ta a matsayin “mace mai matuƙar daraja da girmamawa” a yayin gudanar da taron Addu’ar Ƙasa na 74 (National Prayer Breakfast).

Trump ya faɗi hakan ne a gaban manyan baƙi da shugabanni daga sassa daban-daban na duniya da suka halarci taron, wanda ke gudana duk shekara domin haɗa shugabanni wajen addu’a da tattaunawa kan zaman lafiya, haɗin kai da ƙimar ɗabi’a.

Kalaman shugaban Amurka sun ja hankalin mahalarta taron, tare da nuna irin girmamawa da martabar da Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya ke da ita a matakin ƙasa da ƙasa.

Taron Addu’ar Ƙasa na Amurka na daga cikin manyan taruka da ke haɗa shugabannin siyasa, addini da al’umma, domin ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin al’ummomin duniya.

By Babaji