Kano: Jami’an Hukumar Zaɓe za su fara yi wa ‘yan Yallami rajista a Bichi

Spread the love

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya amince da sanar da al’ummar Bichi jaddawalin yadda jami’an hukumar zaɓe a yankin za su halarci kowace mazaɓa domin saukaka wa mutane mallakar katin zabe a a yankin.

Sule Mai Fata, ya kuma yi kira ga dukkan jama’ar yankin da su mayar da hankali wajen tabbatar da kowa ya mallaki nasa a cikin kayyadaddun lokutan da hukumar zaben ta lamunce a yi wa kowane dan kasa.

A zagayen farko dai a Bichin, mazaɓar Fagolo ce ta rabauta da gudanar da rijistar katin zabe ga mutanen yankin, inda Hukumar Zabe ta yankin ta samu ikon kammalawa da su a yau Alhamis biyar ga watan biyu na shekarar da ake ciki. Kazalika Jami’ar Hukumar Zabe a karamar hukumar Zainab Salihu Mailafiya (Bichi Operation) ta tabbatar da an yi aikin cikin nasara da kwanciyar hankali.

“Al’umar yankin Mazabar Fagolo tare da Kansilan yankin, Hon. Habibu Musa Habibu, sun amshi jami’an Hukumar Zabe ta Bichi hannu bibiyu, an ba su wajen da za su zauna su gidanar da ayyukansu. Saboda haka Alhamdu lillahi kowa ya bi umarni!” Jami’ar Hukumar Zabe (Bichi Operation) Zainab Salihu Mailafiya.

Don haka, a wannan gabar ana shela ga kafatanin jama’ar Mazabar Yallami da jami’an hukumar zaben za su fara yi musu rijistar katin zabe daga gobe Juma’a shida ga watan Fabrairu zuwa sha daya ga watan na Fabrairun da ake ciki na wannan shekara (6/2/2026-11/2/2026). Bisa haka mutanen yankin Yallami ana fatan za su yi fitar dango a wannan mazaba tasu domin mallakar katin zaɓe.

By Babaji