Asibitin ƙwararru na Best Choice ya rage kaso 30 cikin 100 a ayyukan kula da haƙora

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A wani bangare na tausaya wa da kyautatawa al’umma da shugaban asibitin Best Choice Alh Auwal Lawal ya yi, ya bayyana rage kaso 30 cikin 100 na aikin kula da aikin haƙora, asibitin a wata tattaunawarsa da jaridar Alfijir labarai ta wallafa.

Lawan ya jaddada cewa, sabon sashin kula da haƙoran zai duba mara sa lafiya ne a kan wannan ragi tare da ba su shawarwari duba da yanayin da ake ciki na sanyi.

Daga nan Auwal ya jaddada buƙatar da ke akwai ga duk waɗanda ke fama da matsalolin haƙora cewa, asibitin yayi tanadin abubuwan da suka dace game da ƙwararrun likitocin haƙora da suka goge tsawon shekaru, da kuma isassun kayan aikin haƙora na zamani.

Ya jaddada ƙudirin su na share hawayen marasa lafiya inda ya bukace su da kada su yi sanya wajen cin gajiyar wannan tagomashi na ragi da aka samar don kula da lafiyar baki da ta haƙori.

Idan za a iya tunawa, asibitin ya koma babbar helkwatarsa ​​ta dindindin dake shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, da ke kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

Ya ƙara da cewar baya ga ficen da suka yi a fannin kula da mafitsara, asibitin na aiwatar da muhimman ayyukan da suka haɗa da jinyar ƙananan yara (Paediatrics), tiyata (surgery), kula da masu taɓin hankali( psychiatry), ɓangaren haƙori (Dentals), gashin ƙashi ( physiotherapy), sashin kula da cututtukan mata (Gynaecology) da ɓangaren kula da masu ciki da haihuwa, ɓangaren fata (dermatology), manyan ɗakin gwaje-gwaje, kantin magani, da sashin kula da jarirai.

Lawan ya tabbatar da cewa asibitin cike yake da na’urorin kiwon lafiya na zamani irin na ƙasashen duniya, ga kuma tsayayyiyar wutar lantarki.

Hakazalika asibitin bashi da wani reshe ciki ko wajen Kano, mazauninsa na dindindin na shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, da ke kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

By ukarofi