
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi ziyarar barka da sallah ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa dake Kaduna.
Daga cikin waɗanda suka raka shi akwai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, da tsohon gwamnan Benue, Sanata Gabriel Suswam da kuma tsohon gwamnan Adamawa, Muhammad Jibrilla Bindow.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Imo, Achike Udenwa da Aminu Waziri Tambuwal, wanda tsohon gwamnan Jihar Sakkwato ne.
Atiku ya sanar da ziyarar ta kafar sada zumunta inda ya bayyana farin cikinsa bisa hakan, wadda ya ayyana a matsayin abu na musamman a gare shi.
Ana ganin hakan na da alaƙa da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
