Atisayen Fansar Yamma: Za mu ba ku cikakken goyon baya – Gwamnan Zamfara ga Babban Hafsan Tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sake tabbatar wa rundunar sojin Nijeriya ƙoƙarin gwamnatinsa na bai wa jami’anta goyon baya a jihar.

A ranar Juma’a ne gwamanan ya karɓi baƙoncin Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Christopher Musa a Fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.

Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Janar ya Musa ya sanar da sabon atisayen haɗakar jami’ai wanda aka yi wa laƙabi da; ‘Operation Fansan Yamma’ wanda hakan ya kawo ƙarshen baki ɗaya atisaye a yankin Arewa-maso-Yamma.

Sanarwar ta ce, atisayen na ɗauke ne da saƙo mai karfi da ke nuna cewa akwai tsammanin jami’ai a shirye su ke su kawo karshen ta’addanci a shiyyar.

A lokacin da ya ke jawabi, Gwamana Lawal ya yaba wa shugaban ma’aikatan kan ƙoƙarinsa na magance halin rashin tsaro a Nijeriya, ya na mai cewa zuwansa jihar ya ƙara mu su ƙwarin-gwiwa tare da sanya tsammani wa al’umma na kawo ƙarshen munanan ayyukan ta’addancin da suka addabi jihar da ma yankin baki ɗaya.

Ya kuma yaba wa Janar Musa kan amincewa da yin aiki da ma’aikatan sa kai na garuruwa da jami’an wasu hukumomi inda ya ba shi tabbatcin cewa sai da jami’an DSS suka tantance su kafin ɗaukar su a matsayin abokan tafiya.

Dauda Lawal ya ƙara da cewa, a halin yanzu an watsa jami’an zuwa garuruwansu inda nan ne suka fi sani, don haka suna da ƙwarin-gwiwa kan saduakarwar jami’an sojoji na cigaba da hoɓɓasawa wajen kawo ƙarshen taɓarɓarewar tsaro a yankunan.

Ya kuma aika saƙon ta’aziyyarsa game da sojojin da aka rasa a hanyar Gusau-Funtua tare da yi mu su fatan samun rahama.

Haka nan, a ɗaya ɓangaren, Janar Christopher Musa ya yi godiya ga gwamnan kan goyon bayansa ga jami’an sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro a jihar tare da yaba masa kan inganta rayukan al’umma ta hanyoyin ci gaba da aka samu tun bayan hawarsa karagar mulkin jihar.

By Babaji