Audu Baƙo ne aka hana ’yarsa tallafin karatu a lokacin yana gwamna – Sheikh Ibrahim Khalil

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban Majalisar Malamai ta Arewa, Sheik Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Kano, Marigayi Audu Bako, mutum ne mai tsantsar adalci, har ma hukumar tallafin karatu ta jihar ta hana ‘yarsa Scholarship saboda ba ta asalin Kano ba, duk da ya kasance gwamna a lokacin. Ya ce marigayin ya yarda da wannan hukunci cikin natsuwa ba tare da rigima ba.

Shehin malamin ya bayyana cewa duk da ba dan Kano ba ne, Audu Bako ya yi wa Kano ayyuka da suka mamaye tarihin jihar. Ya ce bayan ya bar mulki, jama’a sun nuna masa ƙauna ta hanyar kai masa kaya da tallafi saboda kyawawan halayensa da gaskiyarsa a lokacin mulki.

Haka kuma Sheik Khalil ya ce Audu Bako mutum ne mai bin doka da tsari, wanda bai taba nuna bambanci ko son zuciya ba a mulkinsa. Ya ce wannan ɗabi’a tasa ne har yanzu ake yabonsa a faɗin jihar Kano saboda kyakkyawan tarihi da ya bari.

Ita kuwa Hajiya Zainab Audu Bako, ta roƙi Gwamnatin Kano da Jigawa su mayar da kadarorin da aka ƙwace tun bayan rasuwar mahaifinsu shekaru 45 da suka gabata. Ta ce addini bai amince da riƙe gadon marigayin tsawon lokaci haka ba, kuma lokaci ya yi da za a yi musu adalci.

Ta kuma neman gwamnati ta kafa kwamitin bincike domin tantance duk kadarorin, tare da bai wa iyalan marigayin abin da ya dace a cewar ta, domin a warkar da raunin da suka dade suna ji tun bayan rasuwar mahaifinsu.

By ukarofi