Awaza 2024/2034: UAE ta bayyana ƙudurinta na zuba jari a fannin makamashi, sufuri da ababen more rayuwa

Spread the love

A ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, aka buɗe babban taron Majalisar ɗinkin Duniya karo na uku da ke nazari kan ƙalubalen ƙasashe 32 da ba su da iyakokin ruwa (LLDCs), a birnin Awaza na ƙasar Turkmenistan. Taron ya haɗa shugabannin ƙasa, ministoci, da wakilan manyan hukumomin duniya domin tsara hanyoyin da za su fitar da waɗannan ƙasashe daga ƙangin matsalolin su na cinikayya da ci gaba.

Babban manufar wannan taro mai taken “Inganta Ci gaba Ta Hanyar Haɗin Gwiwa”, shi ne aiwatar da Shirin Awaza na Shekaru Goma (2024–2034) wanda aka amince da shi a watan Disamban 2024. Wannan shiri na da nufin cike giɓin ci gaban tattalin arziki da samun ingantaccen ababen more rayuwa a tsakanin ƙasashen LLDC.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta samu wakilci daga manyan jami’anta, ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi da Ababen More Rayuwa, Suhail bin Mohammed Faraj Al Mazrouei, wanda kuma shi ne Jakada na Musamman na Harkokin Wajen UAE zuwa Turkmenistan.

Al Mazrouei ya bayyana cewa, UAE na goyon bayan wannan taro saboda yana da nasaba da ƙudirinta na inganta ci gaban duniya da kuma bunƙasa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

A cewar Al Mazrouei: “UAE na da niyyar tallafa wa waɗannan ƙasashe da suka takaita daga shiga teku, ta hanyar zuba jari a fannin fasaha, makamashi da sadarwa, domin rage musu wahalhalun da ke tattare da rashin hanyar ruwa.”

A yayin taron, wakilan UAE sun gudanar da ganawa da manyan jami’an ƙasashe masu mahimmanci a fannin ci gaba, ciki har da:

Rashid Meredov, Mataimakin Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Turkmenistan, Abdulkadir Uraloğlu, Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin makamashi, sufuri da zuba jari.

ƙasashen LLDCs na fama da babban koma-baya wajen samun damar yin ciniki, da faɗaɗa fannin masana’antu, saboda rashin iyaka da teku. Hakan na sa su fuskantar tsadar sufuri da nakasu a hanyoyin samun kayayyaki da sabis.

A halin yanzu, ƙasashe 32 masu irin wannan matsala na da jama’a fiye da miliyan 600, inda yawancin su ke cikin Nahiyoyi kamar Afirka da Asiya.

An gina wannan shiri a kan ginshiƙai guda biyar:

1. Sauya tsarin tattalin arziki da ƙarfafa fasaha da bincike.

2. Cinikayya da hadin gwiwar yankuna.

3. Inganta janyoyin sufuri da sadarwa.

4. Rage raɗaɗin canjin yanayi da ƙarfafa juriyar ƙasashe.

5. Aiwana, kula da ayyuka da binciken ci gaba.

Wasu daga cikin muhimman matakan shirin sun hada da:

Kafa Clcibiyoyin binciken noma a matakin yankuna.

Kirkiro da asusun kuɗi na zuba jari a manyan ababen more rayuwa.

Kafa kwamitin Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya kan ‘Yancin Wucewa ta Hanya

Gabatar da shirin WTO na musamman kan matsalolin LLDCs.

Gina kwamitin tattaunawa na UNFCCC don daidaita batutuwan kasuwanci da sauyin yanayi.

Taron LLDC3 a Awaza na ɗauke da makoma mai amfani ga miliyoyin mutane a ƙasashen da suka keɓe. Tare da tsare-tsaren shirin Awaza, duniya na fatan ganin ƙarin haɗin gwiwa da sabbin hanyoyin bunƙasa ƙasa da ƙasa.

By ukarofi