Wata kotun birnin London ta yanke hukuncin ɗauri na tsawon watanni 15 ga Salman Iftikhar, wani attajiri ɗan asalin Pakistan, sakamakon mummunan halin da ya nuna yayin tafiya a jirgin saman kamfanin Virgin Atlantic daga London zuwa Lahore a shekarar 2023. An bayyana cewa Iftikhar ya yi barazana ga ma’aikaciyar jirgi da cewa za a yi mata fyade ta kai ga mutuwa tare da kona ta da wuta, dukkansu a gaban fasinjoji da iyalansa, ciki har da ‘ya’yansa uku.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne bayan da aka ga Iftikhar yana zuba ƙanƙara da hannunsa daga mashayar cikin jirgin ɗin yayin da yake shan giya. Lokacin da ma’aikatan jirgin suka nemi ya daina hakan bisa ƙa’ida, sai ya fara zagin su da kalmomin batsa da kuma zargin wariyar launin fata.
“Kin kira ni alade a gaban kowa,” inji shi ga ma’aikaciyar, ya ƙara da cewa, za a ja ta daga ɗakinta a otal, a yi mata fyaɗe a ƙungiyance sannan a ƙona ta da wuta. Wannan barazana ta firgita matafiyan da ke cikin jirgin, musamman ganin cewa yana tare da matarsa da ‘ya’yansa guda uku.
Alƙalin kotun ya ji cewa Iftikhar ya ƙi kwantar da hankali har lokacin da aka kira ɗaukacin ma’aikatan jirgin domin magance matsalar. Matar tasa har ta kai ga neman gafara a madadinsa, amma ya tureta yana zagin ta. Lokacin da aka sanar da shi cewa za a iya saukar gaggawa a Turkiyya saboda halinsa, sai ya ce, “Ina da mutane ko a nan. Ku sauka mana, ban damu ba.”
Duk da rikicin da ya tayar a sama, da jirgin ya sauka a Lahore ba a kama shi ba. Sai bayan wata guda da rabi a ranar 16 ga Maris, 2024 ne jami’an tsaro suka kama shi a gidansa da ke Iver, Buckinghamshire, a Birtaniya.
Salman Iftikhar na da tarihin aikata laifuka da suka haɗa da dukan jama’a a shekarar 2004 da kuma tuhumar tuƙi cikin maye a 2008, dukkansu na baya. Yana jagorantar kamfanin ɗaukar ma’aikata mai suna Staffing Match, kamar yadda shafinsa na LinkedIn ya nuna.
Ma’aikaciyar jirgin da ta sha wannan wulaƙancin ta shaida wa kotu cewa ta shafe watanni 14 tana fama da damuwa da fargaba, har ta kasa komawa bakin aiki. Wannan ya janyo mata gagarumin rauni na ƙwaƙwalwa da buƙatar kulawar masana lafiya.
Kotun da ta saurari ƙarar ta bayyana cewa, halin da Iftikhar ya nuna “abin ƙyama ne” kuma “ba za a lamunci irin wannan dabbanci da barazana ga ma’aikatan jirgi ba.” Haka kuma, an bayyana cewa gaban fasinjoji da iyalansa ya yi barazanar kashe mutane a otal da ma haddasa firgici a cikin jirgin sama, lamarin da ya saɓa wa doka sosai.
