Yadda ‘hayaƙin janareta’ ya kashe mutum huɗu ’yan gida ɗaya a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mazauna ƙauyen Chatta da ke ƙaramar Hukumar Hawul a jihar Borno sun faɗa alhini sakamakon rasuwar wasu mutum huɗu ’yan gida ɗaya.

Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayaƙin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalinsu.

Majiyoyin da ke ƙauyen sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa waɗanda suka mutun sun haɗa da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu.

Wani ɗan uwar mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan ne a lokacin da ya ziyarci gidan da sanyin safiyar Talata inda ya tarar da gidan gaba ɗaya ba a halin da aka saba gani ba.

“Na zo da misalin ƙarfe 7:00 na safe na yi ta buga ƙofar gidan amma babu wanda ya amsa, sai na shiga damuwa kuma daga ƙarshe dole na ɓalle ƙofar, a lokacin ne na ga gawarwakinsu a kwance a cikin ɗakin,” inji shi.

Ya kuma ce, “Bayan gano lamarin nan da nan na sanar da hukumomin ’yan sanda da ma’aikatan lafiya yadda ba tare da ɓata lokaci ba suka ziyarci wurin inda suka tabbatar da mutuwar dukkan ’yan uwan huɗu.

“Daga baya an kwashe gawarwakin zuwa babban asibitin garin Marama, inda aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawarwaki domin adanawa da kuma tantance musabbabin mutuwarsu.

Mutanen ƙauyen sun bayyana lamarin a matsayin abin da ya dame su kuma sun ce mamatan kafin nan ba su nuna alamun wata rashin lafiya ko damuwa ba kafin mutuwarsu ta farar ɗaya.

Sun ce binciken farko da aka yi a wurin ya nuna babu wani alamun tashin hankali, amma mazauna yankin na zargin yiwuwar kamuwa da guba ko shaƙar gurɓatacciyar iska daga wani injin janareta da suke amfani da shi.

Rundunar ’Yan Sandan jihar ta bakin Kakakinta, ASP Nahum Daso ta ce tuni an fara bincike don gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen.

By ukarofi