
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sakataren yaɗa labaran Jam’iyyar APC na Ƙasa, Felix Morka, ya yi watsi da iƙirarin cewa wai ministocin da ke ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun biya biliyoyin kuɗaɗen nairori kafin aka naɗa su a muƙaman jagorantar ma’aikatu.
Morka ya yi watsi da wannan iƙirari ne a wata hira da gidan talabijin na Arise yayin shirin Prime Time a ranar Laraba, inda ya ce kalaman, waɗanda aka jiyo su a bakin Alwan Hassan, wanda Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ne, na magana ne kan gwamnatocin baya ba ta yanzu ba a ƙarƙashin mulkin Tinubu. Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci sun biya biliyoyin nairori domin neman a naɗa su a muƙaman minista, sannan sun fara aiki ne da nufin dawo da abin da suka kashe kafin zuwa matsayin.
Ya yi wannan zargi ne a wata hira da Charles Aniagolu a gidan talabijin na Arise a wani daren Alhamis yayin bayar da kariya ga salon Tinubu na gudanar da kuɗaɗen harajin gwamnati da waɗanda ake kashewa.
Saidai, Morka ya ce kalaman na Hassan masu tayar da ƙura tarihi ne ba akan ministocin da ke aiki a gwamnatin Tinubu ba. A cewarsa, bayan tattaunawar, ya yi hira da Alwan Hassan domin fahimtar ainihin yadda zancen yake, inda ya ce masa ba ya nufin gwamnatin Tinubu, amma ya yi maganar ne a lokacin da ya ɗauko wani tarihi na tsokaci kan halin da ministoci suka tsinci kansu a gwamnatocin baya.
Morka ya bayyana cewa, ana yin naɗe-naɗe a ƙarƙashin Tinubu ne bisa la’akari da cancanta, ƙwarewa da jajircewa wajen sauke nauyi a madadin amfani da salon tatsar kuɗaɗe domin bada muƙami.
Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci sun biya maƙudan kuɗaɗe domin samun matsayi, inda ya yi iƙirarin cewa hakan bai taƙaitu ga APC ba kaɗai, sannan ya ce ministoci na daga cikin jami’an gwamnati da suka fi lalacewa a gwamnatocin da suka gabata, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen gaza warware matsalolin rashawa acikinsu musamman ministoci.
