Ba don ƙananan masana’antu ba, da kaso 80 na ƴan Nijeriya ba su da aikin yi – Shettima

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yace kashi 80 na ayyukan yi ya ta’allaƙa ne sakamakon yaɗuwar ƙananan masana’antu (MSME) acikin al’umma a Nijeriya wanda rashin hakan ka iya haifar da rashin aikin yi ga wannan kason.

Shettima ya faɗi haka ne a Markudi, babban birnin jihar Benue a lokacin buɗe gidan kayan ƙawa na jihar da hukumar buga takardu da wallafa su ta jihar (BPPC) inda ya ce ƙananan masana’antu ginshiƙi ne ga tattalin arziƙin ƙasa don haka gwamnatin shugaba Tinubu ke ƙoƙarin haɓaka su.

Ya ce, abu ne mai wahala tattalin arziƙin Nijeriya ya samu ci gaba ba tare da MSME ba.

A lokacin da ya ke magana ta ɓangaren Mataimakin shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, Shettima yace gidan kayan ƙawan da aka buɗe a Benue shi ne mafi girma daga cikin biyar da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da buɗe su a Nijeriya.

Ya ce, gidan zai zama cibiyar ƙwarewa a arewacin Nijeriya da kuma ɗaukaka martabar kayan al’adun jihar da kuma samar da ayyukan yi a kowace shekara da adadinsu ya ƙai 48,000 a cikin al’umma.

Game da hukumar buga takardu da wallafa su ta BPPC, gwamnan jihar, Hyacinth Alia yace an sabunta shi ne tare da zuba masa kayan aiki ta hanyar haɗaka da ‘Public Private Partnership’ da gwamnatinsa ta yi don bai wa jama’a damar cin gajiyarsa da kuma samar da ayyukan yi a gare su.

By Babaji