Ba mu cimma masu zuba jari miliyan 10 ba – Ɗangote

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Kamfanin Masana’antun Ɗangote (DIL) Aliko Ɗangote, ya bayyana cewa, shirin raba hannayen jarin kamfanin na IPO na matatarsu ya rasa cimma harinsa na janyo masu zuba jari guda miliyan 10, duk da cewa an samu miliyoyin al’umma da suka shiga cikinsa. Ya ce, hakan ya faru ne sakamakon ƙarancin lokacin da aka bayar da siyan hannayen jarin da kuma matsaloli da wasu suka fuskanta wajen samun damar siya.

Da yake jawabi a taron shekara-shekara na Mata a Gudanarwa, Kasuwanci da Hidimar Al’umma (WIMBIZ) karo na 25 a Legas, Ɗangote ya ce har yanzu ba a samu ainihin adadin masu zuba jarin da ake so ba, amma ya ce an samu gagarumar nasara wajen shigar jama’a da dama.

Ya bayyana cewa, Matatar Ɗangote ta samu zuba jari daga miliyoyin mutane, wanda hakan na da muhimmanci a tsare-tsaren kasuwancin Afirka da matakin ƙasa-da-ƙasa, yana mai cewa a lokacin da bankin GT ya siyar da nasa hannayen jarin, mutane 200,000 aka samu, amma IPOn su ya samu miliyoyin mutane.

Ɗangote ya kuma bayar da misali da kamfanin Safaricom na Kenya, wanda ya samu ƙasa da mutum 900,000 da suka zuba jari, da Saudi Aramco da ya samu kusan mutane miliyan biyar bayan bai wa ‘yan duka ƙasashen duniya damar shiga.

Shirin IPO na Ɗangote ya hari bayar da hannayen jari biliyan 4.1 akan N525 kowanne, inda kowane mutum ke da damar siya hannu 10 mafi ƙaranci. An fara shirin ne a ranar 14 ga Satumba, sannan aka rufe a ranar 27 ga Oktoba, 2026.

By Babaji

Leave a Reply