Babban jami’in rediyon Freedom da Dala FM, Shehu Ɗalhatu ya rasu

Spread the love

Inna Lillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un!

Cikin alhini mu ke sanar da rasuwar ɗaya daga cikin daraktocin Hukumar Gudanarwar Rukunin Tashoshin Freedom Rediyo da Dala FM, Alhaji Shehu Ɗalhatu.

Marigayin ya rasu ne a yammacin Jumu’ar nan a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, inda aka bada umarnin yin jana’izarsa.

Ana karɓar gaisuwa a gidan Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu da ke Hotoro Kwanar Maggi, a Kano.

Mu na addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma ba mu haƙurin jure wannan rashi.

Sanarwa daga Hukumar Gudanarwa ta Freedom Rediyo.

By Babaji