
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Sakataren Sashen Ayyuka na Musamman na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Shehu Yahaya Jalam, ya rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya yayin da yake gudanar da aikin Hajji.
Jalam, wanda kuma shi ne Turakin Dawakin Misau, ya rasu ne a safiyar Lahadi bayan rashin lafiya yayin aikin Hajji a lokacin da yake tare da tawagar mahajjatan Jihar Bauchi, kamar wata sanarwa ta bayyana.
Tuni dai gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana alhini da jimami akan rashin babban jami’in, tana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga ma’aikatar gwamnati da kuma ofishin da yake yi wa aiki.
Sanarwar ta kuma ce marigayin yana rike da sarautar gargajiya ta Turakin Dawakin Misau, kuma an san shi a matsayin ma’aikacin gwamnati mai himma da kwazo wajen aiki.
Ana sa ran za a yi masa jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci a Saudiyya, yayin da ake cigaba da aika saƙonnin ta’aziyya daga jami’an gwamnati da abokan aiki da kuma ɗaukacin al’umma.
