Zaɓen fidda gwanin APC: An kada ɗan tsohon Shugaban Jam’iyya da Kakakin Majalisar Nasarawa

Spread the love

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Danladi Jatau, ya rasa damar tsaya wa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Keffi/Karu/Kokona bayan shan kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

Rt. Hon. Danladi Jatau ya samu ƙuri’u 5,873 ne kacal, yayin da abokin takararsa, Hon. Daniel Ogazi, ya lashe zaɓen da kuri’a 13,083.

Jaridar Punch ta ce haka kuma wasu ‘yan majalisar wakilai biyu masu ci sun rasa tikitin komawa takara bayan kammala zabukan fitar da gwani a cikin lumana a mazabunsu daban-daban.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan majalisar da abin ya shafa sun hada da Mohammed Abdulmumini Ari mai wakiltar Nasarawa/Toto da kuma Jeremiah Umaru mai wakiltar Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba.

Da yake sanar da sakamakon zaben a Lafia, shugaban kwamitin zaben fitar da gwani na APC na Majalisar Tarayya a Nasarawa, Musa Shuaibu Guri, ya ce an gudanar da zaben bisa tsarin kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin zabe da kuma ka’idojin jam’iyyar APC.

Ya bayyana cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci a dukkan kananan hukumomi 13 na jihar, saboda haka babu wanda aka zalunta.

Daga cikin wadanda suka samu tikitin takarar APC akwai Mohammed Al-Bashir na mazabar Nasarawa/Toto, Daniel Ogazi na Keffi/Karu/Kokona, da Tony Bala Shammah na Akwanga/Nasarawa Eggon/Wamba.

Haka kuma Mohammed Al-Makura ya zama dan takarar APC na mazabar Lafia/Obi bayan da abokin hamayyarsa Isaac Kigbu ya janye daga takarar tun ranar Asabar.

Sai dai Guri ya bayyana cewa har yanzu ana tattara sakamakon mazabar Awe/Doma/Keana, inda za a sanar da shi nan gaba.

By Babaji