
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakta Kaumi Zulum, wanda ɗan uwan Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ne, ya lashe zaɓen fidda gwani a jam’iyyar APC na mazaɓar tarayya ta Dikwa/Konduga/Mafa a Majalisar Wakilai.
Baturen zaɓen yankin, Jones Erue a wani taron manema labarai a Maiduguri, ya ce Zulum ne wanda ya lashe zaɓen ba tare da abokin karawa ba.
Haka kuma, Mista Erue ya sanar da Fati Alƙali a matsayin ‘yar takara kujerar Majalisar Wakilai ta mazaɓar tarayya ta Mobbar, Guzama, Abadam da Kukawa.
Sannan, ya sanar da Usman Zana a matsayin ɗan takarar APC na Magumeri/Kaga/Gubio.
Kazalika, Erue ya ayyana Ahmed Jaha a matsayin ɗan takarar APC a mazaɓar Gwoza/Chibok/Damboa.
Kamar haka ne ya sanar da zaɓen Askira-Uba/Hawul a matsayin wanda ba a kammala ba.
