Yusuf Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar sanata na APC a Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan tsohon shugaban ƙasa Yusuf Buhari ɗan takarar jam’iyar APC a majalisar wakilai a zaɓen 2026 ya yaba da yadda jam’iyar ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar majalisar dattijai na shiyar Daura.

Yusuf Buhari ya yi wannan yabo ga manema labarai a wata makaranta firamare a garin Daura lokacin da ya zagaya wurin da aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar jam’iyar.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar katsina Rt Hon Nasiru Yahaya Daura da Abdulkarim Aliyu AK suka fafata a neman tsayawa takarar kujerar majalisar dattijai na shiyar Daura.

Tsohon Sanata Hadi Sirika da Shehu Audu da sanata mai ci yanzu sanata Nasiru Sani Zangon Daura suka janye takarar su.

Shima ɗan takarar kujerar Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya nuna gamsuwar sa da yadda aka gudanar da zaɓen a musamma a wuraren da ya ziyarta.

Ya nuna jin daɗin kan yadda ya ‘yan jam’iyar su ka fito ƙasa ƙuri’a zaɓen fidda ɗan takarar,inda ya ce yana da yaƙinin zai lashe zaɓe.

Shiyar Daura na da rumfar zabe 159 a ƙananan hukumomi 12.

Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua na shiyar Katsina da Sanata Muntari Dandutse na shiyar Funtua ba su da hamayya za su sake shiga zaɓen kujerar ƙarƙashin jam’iyar APC a jihar Katsina.

By ukarofi