Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ɗora wa gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 alhakin gudanar da ayyukan raya ƙasa a matakin ƙasa, inda ya ce cin gashin kan harkokin kuɗi da aka bai wa ƙananan hukumomi ba wani yunƙuri ne na kwace mulkin ɓangaren daga hannun gwamnoninnba.
Shugaban ya ce, shugabancin gwamnoni a matakin ƙasa shi ne jigon samar da wadataccen abinci, wadatar tattalin arziki da ci gaban ƙasa cikin sauri.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da mambobin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak suka kai masa gaisuwar sabuwar shekara a gidansa na Ikoyi da ke Legas.
Shugaban ya jaddada muhimmancin ci gaban ƙasa tare da kawar da jita-jitar rashin jituwa da gwamnoni.
“Akwai jita-jita cewa mun samu rashin jituwa a kan cin gashin kan ƙananan hukumomi. A’a, kawai burinmu shi ne kawo cigaba a ƙananan hukumomi. Babu wanda yake so ya karɓe su daga gare ku, amma muna buƙatar haɗin gwiwa. Mu yi shi tare kuma mu tabbatar da cewa Nijeriya ta gyaru,” inji Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar.
Tinubu ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi domin tunkarar ƙalubalen da ke addabar ƙananan hukumomi da suka haɗa da cin gashin kan ƙananan hukumomi, samar da ayyukan noma, da kuma daidaita ayyukan kuɗin.
Shugaba Tinubu ya buƙaci gwamnonin da su ba da fifiko wajen bunƙasa noma a matsayin hanyar samun daidaiton tattalin arziki.
