Fasto ya bindige matashi bayan buga ‘knockout’ na sabuwar shekara a coci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani babban limamin cocin Katolika ya harbe wani matashi har lahira bayan da ya tayar banga ta ‘knockout’ a cocin.

Lamarin ya faru ne a yayin taron sabuwar shekara da aka gudanar a ranar 1 ga Janairu, 2025, a Amaimo da ke yankin ƙaramar Hukumar Ikeduru ta Jihar Imo.

Shaidu sun yi iƙirarin cewa, matashin yana bikin sabuwar shekara da wasan banga a wajen harabar cocin lokacin da limamin cocin ya tunkare shi. Rikicin ya yi ƙamari, wanda ya kai ga harbe-harbe.

A wani saƙon da aka wallafa a shafin Facebook, ‘For The Loɓe Of Anambra,’ a ranar Laraba, ta ruwaito wasu shaidun gani da ido, sun ruwaito cewa bayan da mamacin ya tashi bugun bangar ta ɗaya, “limamin cocin, wanda har yanzu ba a bayyana ko wane ne ba, ya ɗauki bindiga ya harbe shi.

“Lamarin ya jefa al’umma cikin firgici da alhini, inda mazauna yankin suka nuna ɓacin ransu tare da neman a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.”

Lamarin dai ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, inda mazauna yankin suka yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da cikakken bayani ba ko kuma bayar da sanarwa a hukumance dangane da lamarin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yan sandan Imo, Henry Okoye, ya shaid awa jaridar The Nation a ranar Alhamis cewa: “An kama limamin cocin, kuma an gano gawar yaron an ajiye shi a ɗakin ajiye gawa na Atta Ikeduru.”

By ukarofi