Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya miƙa goron gayyata ga tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, domin zuwa matatar mai ta Fatakwal, saboda tabbatar da matsayinta na gudanar da aiki.
Wannan ya biyo bayan hirar da Obasanjo ya yi da gidan talabijin na Channels ne kwanakin baya, inda ya bayar da misali da shawarar kamfanin Shell Petroleum Deɓelopment Company (SPDC) da ke nuna matatar ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba.
A cewar tsohon shugaban, Shell da aka tuntuɓa, don samun daidaito a matatar, ya bayyana damuwarsa game da cin hanci da rashawa da ke hana ayyukanta. Obasanjo ya kuma yi zargin cewa, NNPC na yaudarar ’yan Nijeriya game da ayyukan matatar.
Yayin da ya ke mayar da martani kan iƙirarin na Obasanjo, Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Mista Olufemi Soneye, cikin girmamawa ya gayyaci tsohon shugaban ƙasar da ya ziyarci matatar, inda ya jaddada ƙudirin kamfanin na yin gaskiya da riƙon amana.
Soneye ya ce: “Bugu da ƙari, muna miƙa goron gayyata ga Shugaba Obasanjo, domin ya zagaya matatun mai da aka gyara, domin gane wa idonsa irin ci gaban da aka samu a ƙarƙashin sabon kamfanin NNPC Limited.”
Soneye ya kuma gayyaci Obasanjo da ya bi sahun hukumar ta NNPC a ƙudirinsa na tabbatar da tsaron makamashin ƙasar.
“Muna gayyatar mai girma tsohon shugaban ƙasarmu da ya zo tare da mu a wannan ƙoƙarin da muke ci gaba da samar da tsaron makamashi ga al’ummarmu da kuma samar da fa’ida ta zahiri ga ‘yan Nijeriya.
“Hikimarsa da ƙwarewarsa suna da ƙima, kuma muna ba shi tabbacin cewa za a yi maraba da shawararsa a koyaushe,” inji shi.
Soneye ya bayyana cewa, NNPCL ba wai kawai ya gudanar da aikin gyara matatar man ba ne, amma ya fara yin garambawul ga matatar.
Ya ce: “a wani ɓangare na wannan sauyi, kamfanin NNPC Limited ya wuce mai da iskar gas ya zama kamfanin haɗaka da makamashi.
“ɗaya daga cikin manyan nasarorin da muka samu shi ne na sake gyara kamfanin matatar man Fatakwal (PhRC) da matatar mai na Warri.
Ya ƙara da cewa, NNPCL ya tashi daga zama kamfani na gwamnati zuwa wani kamfani mai zaman kansa wanda ke da iyakacin alhaki.
