Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Nijeriya baki ɗaya.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu.
Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha.
“Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini ba ne. Ya kamata mutane su duba ma’anar kisan kare addini ta Majalisar ɗinkin Duniya.”
Ya kuma ce babu wani jihadi da ake yi a kowane ɓangare na Nijeriya, ko da yake ƙungiyoyin ’yan ta’adda kamar Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas, suna iƙirarin jihadi.
“Babu wani jihadi a Nijeriya,” inji Alia.
“A matsayina na Fasto kuma gwamna, ni ne zan fara yin magana idan hakan na faruwa a jihata ko a wani ɓangare na ƙasar nan.”
Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Nijeriya.
Amurka ta taɓa sanya Nijeriya a cikin jerin “ƙasashen Masu Matsala ta Musamman” saboda cin zarafin addini, amma gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi.
Kiristoci da Musulmai duka sun sha wahala sakamakon rashin tsaro, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane.
Gwamna Alia, ya ce ya gana da ofishin jakadancin Amurka don bayyana yadda halin tsaro yake a Binuwai.
“Na bayyana cewa babu kisan ƙare addini a Nijeriya, musamman a Binuwai. Ma’anar Majalisar ɗinkin Duniya ba ta dace da yanayin nan ba,” inji shi.
Jihar Binuwai ta jima tana fuskantar matsalolin da suka shafi kisan jama’a da sace mutane.
Bayanai sun nuna cewa sama da mutum 800 sun mutu, yayin da aka sace kusan mutum 400 cikin shekaru biyu da suka gabata.
A watan Yuni, aƙalla mutum 100 ne suka mutu a hare-haren da ’yan ta’adda suka kai a ƙaramar Hukumar Guma.
