Lokaci ya yi da Nijeriya za ta daƙile yawan sace-sacen ɗalibai

Spread the love

Tsaron makarantu a Nijeriya ya shiga wani sabon yanayi mai tayar da hankali. Shekaru goma sha biyu da suka gabata sun fara nuna mana haɗarin da ke tattare da barazanar ta’addanci da sace-sacen ɗalibai, amma abin da ke faruwa a yau ya zarce nan; yawan hare-haren da ake kaiwa makarantu ya koma tamkar sabon al’ada. Harin da aka kai kwanan nan a Jihar Kebbi — inda wasu miyagu suka kutsa makarantu suka yi awon gaba da yara masu neman ilimi — ya ƙara bayyana girman matsalar da ke gabanmu. Wannan lamari bai kamata ya ci gaba da faruwa ba a ƙasar da ke da arziki, al’ummar da ke da buri, da gwamnati da ke da nauyin kare rayuka da dukiyoyi.

Hukumomi a jihar Kebbi, Arewa maso Yammacin Nijeriya sun tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a Makarantar Sakandiren ’Yan Mata da ke garin Maga, inda suka kashe aƙalla ma’aikaci ɗaya da sace ɗalibai.

Lamarin ya faru ne da asubahin Litinin lokacin da ɗaliban ke shirin tashi sallar asuba.

Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗalibai, waɗanda ba a riga an tantance adadinsu ba.

Wannan ne hari na baya-baya da irin waɗannan ’yan bindiga suka riƙa kaiwa a makarantu suna sace ɗalibai a jihohi daban-daban na ƙasar, musamman yankin arewacin ƙasar mai fama da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Makarantar kwanan ta ‘yan mata na a garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar.

A ko ina cikin duniya, makaranta na nufin mafakar ilimi, amintaccen wuri domin gina gobe. Amma a wasu yankunan Nijeriya, makaranta ta zama wurin tsoro — inda iyaye ke jinjina rai kafin su ajiye yaransu, sannan su ci gaba da addu’a har lokacin da za su dawo gida. Wannan ba halin da ya dace mu bar al’umma a ciki ba ne. A matsayinta na ƙasa mai yawan matasa, Nijeriya za ta yi hasara mai tsanani idan al’ummar da ta fi yawa ba ta da tsaro a muhimman muhallansu na karatu.

Hare-haren da ake kaiwa makarantu, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sun shaida mana cewa matsalar ba ta taƙaita ga ƙananan hari na ɓarayin shanu ko ‘yan fashin daji kaɗai ba. Ta koma wani gagarumin tsarin laifi mai nufin karya garkuwar ilimi ta hanyar tsoratarwa, tsare ɗalibai, da neman kuɗaɗen fansa. Wannan mummunan salon da miyagun suka sakawa gaba ya haifar bala’i, fargaba, kashe kwarin gwiwa, da durƙusar da burin iyaye da yara.

Sai dai a daidai wannan lokaci mai wahala, ya kamata a yaba wasu matakai da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka—duk da cewa akwai sauran tazara mai nisa. Gwamnatin tarayya ta bayyana ƙudirinta na ƙarfafa tsaron makarantu, musamman bayan harin Kebbi. Wannan ya nuna cewa an fara fahimtar cewa tsaron makarantu ba kawai aikin jiha ba ne, ko na hukumomin tsaro kaɗai, illa babban aikin ƙasa da ke buƙatar dabaru, tsari, da haɗin kai.

Akwai buƙatar a fito fili a ce: gwamnati ta nuna jajircewa ta hanyoyi daban-daban. Akwai ƙarin rundunar sojoji a yankunan da ake fama da matsala, akwai ƙaddamar da shirin Safe School Initiatiɓe, akwai kuma ƙoƙarin kafa tsarin sa ido na zamani a wasu jihohi da ke cikin mawuyacin hali. Ayyukan ba su kai ga matakin da ake buƙata ba tukuna, amma ba za a yi watsi da matakin da aka fara kaiwa ba. A wannan lokaci ba abin da ya fi muhimmanci kamar ƙarfafa waɗannan matakai, da tabbatar da cewa su zama aiki mai ɗorewa maimakon zantukan siyasa kawai.

Duk da irin waɗannan ƙoƙari, akwai abubuwa uku da ya zama wajibi gwamnati ta duba da sabunta su matuƙa domin kawo babban sauyi.

Da fari, ya zama wajibi a sake fasalin tsarin tsaron makarantu. Tsaro a yau ba ya buƙatar bindigogi kawai. Yana buƙatar bayanan sirri, na’urorin ganowa, sadarwa ta zamani, da sa ido mai inganci. Abin da ya faru a Kebbi ya sake nuna mana cewa makarantunmu a yankunan karkara sun kasance cikin yanayi mai sauƙi da ke baiwa miyagun damar kai hari cikin sauƙi. Wata makaranta da ke sarara ba tare da katanga, amintaccen ɗakin koyarwa, ko mai gadi na gaske ba, ba ta da wata kariya daga barazanar da ake fuskanta a wannan zamani.

Na biyu, akwai buƙatar ƙara inganta hulɗa da al’umma (community engagement). Yawancin hare-hare kan faru ne saboda makwabta ko mazauna yankin ba su da ikon ba da rahoton abin da ke faruwa ko za a faru da shi. ƙauyuka dole su riwa gadin kansu, amma su yi hakan cikin tsarin doka, jagoranci, da horo. Gwamnati za ta iya kafa rundunar sa-kai na kariya ga makarantu (community school guards) masu samun horo daga jami’an tsaro, ba masu wuce gona da iri ba.

Na uku, dole a hukunta waɗanda ke ɗaukar nauyin waɗannan miyagu. Matsalar sace-sacen ɗalibai ba ta ƙare da ‘yan bindiga da ke cikin daji ba. Akwai masu saye da sayarwa, akwai masu ba da kayan aiki, akwai masu bai wa ‘yan ta’adda bayanai. Dole gwamnati ta ci gaba da warware wannan cibiyar laifi kamar yadda take ƙoƙarin yi, ta hanyar amfani da bayanan sirri da sare hanyoyin kuɗi da hulɗa da suke dogaro da su. Wannan wani ɓangare ne da gwamnatin tarayya ke ƙara sa himma a cikinsa, kuma ya dace a ci gaba da yaba irin wannan jajircewa.

Sai kuma batun iyaye da al’umma. Yana da muhimmanci mu fahimci cewa tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne. Lokaci ya yi da al’umma za su fara kai tsaye wajen kare makarantun su, taimakawa wajen bayar da bayanan sirri, da kuma tabbatar da cewa duk wani abu da ba a saba gani ba ana sanar da hukumomi cikin gaggawa. Duk da cewa gwamnati ce ke da babban nauyi, al’umma ita ce idanu da kunne na yankunan da ke fuskantar barazana.

Idan muka koma ga yadda harin Kebbi ya faru, za mu ga yadda miyagu suka shiga cikin dare, suka ɗauki ɗalibai ba tare da wata matsin lamba ba. Amma da yawa daga cikin su an ce sun zo daga kan iyaka tsakanin jihar, hanyar da ke fama da gagarumar matsalar tsaro shekaru da dama. Wannan na nuna mana cewa sai an inganta tsaron iyakoki, an ƙara yawan jami’an tsaro, da kuma samar da na’urorin sa ido—kamar yadda gwamnati ta fara aikatawa—a nan ne za mu fara ganin sauyi mai ɗorewa.

A gefe guda kuma, akwai faɗakarwa mai muhimmanci: duk da cewa gwamnati na ƙoƙari, bai kamata a jingina komai a kan hakan kawai ba. Akwai mamaki yadda wasu makarantu ke ci gaba da kasancewa ba tare da ma’aikatan tsaro a kowace rana ba; yadda iyaye ke kai yaran su makarantu da ke da katanga mara kyau, ko babu kwaɗon tsaro, ko babu masu gadi da aka horar. Idan muka yi watsi da irin waɗannan bayanai ƙanana, za su kai ga babbar matsala kamar yadda aka gani a Kebbi da sauran makarantu

Haƙiƙa, Nijeriya na cikin wani mawuyacin hali amma kuma na cikin wani lokaci da ke buƙatar ƙarfin halin gwamnati da al’umma. Ya kamata mu kasance cikin yanayi na gaskiya: ba za mu iya magance matsalar nan take ba. Amma idan an daɗe ana cusa tsari mai ƙarfi, an yi aiki ba tare da siyasa ta shigo ba, sannan an samu haɗin kan al’umma, za mu kai ga wani matakin da makarantu za su sake zama mafakar ilimi maimakon wuri mai haifar da tsoro.

Duk da haka, ya dace mu yabi gwamnatin tarayya bisa ƙoƙarinta wajen ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan iyakoki da ake fama da hare-hare, ƙaddamar da sabbin manufofin tsaron makarantu, da kuma jajircewar da ta nuna wajen mayar da batun tsaron yara kan gaba. Waɗannan matakai suna nuni da cewa gwamnati na fahimtar girman matsalar, kuma ta ɗauki hanyar da ta dace—ko da kuwa akwai sauran aiki a gaba.

A ƙarshe, idan har Nijeriya za ta yi nasara, dole gwamnati da al’umma su gane cewa yaran da ake sacewa ba yara ne na Kebbi ko Kaduna ko Katsina kaɗai ba—yaran Nijeriya ne. Kuma duk ɗaya yake a matsayinsu: gobe ce suke gina mana. Idan muka sallama su ga barazanar miyagun, to muna sallama makomar ƙasa baki ɗaya ne.

Lokaci ya yi da Nijeriya za ta ce: “Sace-sacen ɗalibai ya isa, ba za mu ƙara lamunta ba.”

By ukarofi