
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya, Ɗanjuma Goje ya bayyana cewa babu wani rikici a tsakaninsa da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio bisa abinda ya faru a yayin zamansu na ranar Talata, yana mai bayyana al’amarin a matsayin wani ɓangare na ayyukansu.
Goje ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar na ranar Laraba, wato kwana ɗaya bayan ya ƙalubalanci Akpabio bisa abin da ya kira da ‘saɓa aikin majalisa’.
Sanatan ya ce abinda ya yi yana kan doka, saidai wani sashi na ƴan jarida bai fahimci abinda yake nufi ba sakamakon ruwaito al’amarin ta wata fuska.
“Abinda ake magana shi ne bada gudumuwa ta ɓangarena a matsayin gogaggen ɗan majalisa domin tabbatar da majalisar ta bi dokokin. Babu wata manufa ta raɗin kai da ke kishiyantar shugaban majalisar ko kowane sanata”, inji Goje.
Ya kuma roƙi ƴan jarida da masu amfani da kafafen Soshiyal Mediya da su gyara manufar furucin nasa duba da yadda al’umma suka fahimci al’amarin.
A nasa ɓangaren, Sanata Godswill Akpabio ya amshi bayanin Goje hanu biyu-biyu, sannan ya yi kira da a riƙa ruwaito labarai cikin ƙwarewa.
“Ina fata za su ji cewa babu faɗa a Majalisar Dattawa kuma dukkan mu ɗaya ne”, inji Akpabio, yana mai jaddada haɗin kan majalisar.
Jawabin na zuwa ne ƙasa sa’o’i 24 da majalisar ta ɗauki ɗumi a yayin zaman da ta saba na ƴaƴanta sakamakon saɓanin fahimta akan bin dokokinta.
A yanzu sanatocin biyu sun wayar da kan jama’a game da cewa babu wani rikici a tsakaninsu kuma al’amarin da ya faru yana bisa tsari.
