
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) ta amince da ware Naira biliyan 100 a matsayin kuɗin gyaran cibiyoyin horon ƴan sanda da wasu hukumomin tsaro a Nijeriya.
Hakan na na nufin har zuwa hukuncin da Shugaba Bola Tinubu zai yi a kai bisa la’akari da shawarwarin da kwamitin majalisar ya bayar na duba matakin wuraren horon aikin ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin Nijeriya.
A zamanta na 154 da aka gudanar a ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Maitaimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, NEC ta kuma amince da Naira biliyan 2.6 na hidindimun shawarwari game da ayyukan.
Tun a watan Oktoba ne Shugaba Tinubu a zama na 152 ya nemi a yi wa cibiyoyin horon kwaskwarima.
Shugaban ƙwarya-ƙwaryar kwamitin NEC kuma Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mba ya bayyana halin da cibiyoyin suka tsinci kansu na neman gyara tun da jimawa, lamarin da ya sa ya za wajibi a ba su kulawar domin inganta ayyukansu ga tsaron ƙasa da al’umma.
Bayan gabatar da batun ne sai Maitaimakin Shugaban Ƙasar Kashim Shettima ya jaddada ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na warware matsalolin cibiyoyin a gwamnatance.
Ya kuma buƙaci gwamnoni da su tabbatar da aiwatar da gyare-gyaren harkar tattali a ƙarƙashin jagorancinsu ta yadda rayukan al’ummar Nijeriya za su inganta a dalilin haka.
