Remi Tinubu ta bai wa nakasassu 250 tallafi a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Uwargidan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa tattalin arziki ga nakasassu 250 a ƙarƙashin shirinta na inganta rayuwar alumma watau Renewed Hope Initiative, a jihar Zamfara.

Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin da aka gudanar a sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau yau Laraba, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa shirin zai samar da tallafin haɓaka kasuwanci da bayar da zunzurutun kuɗi Naira N200,000 ga kowane nakasashshe inda kowace jiha da kuma babban birnin tarayya za a baiwa nakassassu 250.

Ta ƙara da cewa manufofin shirin shine tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa su sake haɓaka kasuwancinsu don ƙarfafa masu su samun hanyoyin kuɗin shiga.

A cewarta, Nijeriya na ƙara ƙarfi idan aka bai wa kowane mutum damar bayar da gudummawa mai ma’ana.

Uwargidan Shugaban ƙasar Sanata Oluremi Tinubu, wacce matar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta wakilta a wajen ƙaddamar da shirin, ta bayyana cewa kowace jiha da babban birnin tarayya da ƙungiyar matan jami’an tsaro da ‘yan sanda za su sami Naira miliyan hamsin N50,000,000 domin a raba su a yankunansu.

Ta bayyana cewa jimillar mutane 9,500 ne a cikin masu buƙata ta musamman a faɗin Najeriya za su amfana da shirin, wanda ya kai Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari tara.

A cewarta, shirin ya yi daidai da ajandar sabunta ƙasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wacce ke da ƙudirin bunƙasa ci gaba ta hanyar tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da aka bari a baya, musamman waɗanda ake yawan yin watsi da buƙatun su.

Ta ƙara da cewa wannan wani ɓangare ne na shirinta na sabunta hanyoyin tattalin arziki don tunawa da ranar nakasassu ta duniya.

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, Shirin Sabunta Ƙasa watau Renewed Hope Initiative, an tallafawa mata ‘yan kasuwa da ƙananan ‘yan kasuwa sama da 100,000, ciki har da nakasassu, tare da tallafin kuɗi kai tsaye don bunƙasa kasuwancinsu”.

“Shirin ya kuma nuna jajircewarmu wajen inganta rayuwa ta hanyar shiga tsakani a fannoni daban-daban, musamman noma, ƙarfafa tattalin arziki, Ilimi, lafiya, da walwalar jama’a da nufin inganta rayuwar iyalai a faɗin ƙasarmu.” Remi Tinubu ta ƙara da cewa.

Uwargidan Shugaban Ƙasa Remi Tinubu ta kuma yaba wa matar Gwamnan Jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda Lawal saboda goyon bayan da take bai wa Shirin Renewed Hope Initiative ta wajen aiwatar da tallafawa alummar jihar musamman marasa galihu a fannoni daban daban.

Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga waɗanda suka amfana da wannan dama da su yi amfani da ita yadda ya kamata don rayuwar su ta inganta.

By ukarofi