
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da rahotannin da ke zargin yunƙurin juyin mulki ga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tana mai jaddada biyayyar jami’an sojoji ga gwamnatin.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare a wata hira da gidan talabijin na TVC ya ce babu wani abu mai kama da haka a ko’ina a faɗin ƙasar.
Ya ce, gwamnatin ta yanzu tana goyon bayan matsayar rundunar sojoji, wadda ta musanta samun wani abu mai kama da haka a ƙasar.
Ya kuma ce, rundunar sojojin tana cigaba da zama mai aikin kare daraja da haɗin kan Nijeriya bisa umarnin da dokokin ƙasa ta ba su.
Haka kuma, ya jaddada cikakkiyar yarda da aikinsu bisa ƙwarewa daga Shugaba Tinubu da yadda doka ta ba su ikon kula da tsaron ƙasa.
A kwanan nan ne sojoji suka kai samame gidan tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur na gwamnatin marigayi Buhari kuma tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, wato Timipre Sylva da ke Abuja bisa zagin sa da hannun a zargin juyin mulkin.
