Majalisar Dattawa ta tabbatar sababbin jagororin tsaro

Spread the love

A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sababbin hafsoshin rundunar soji da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Majalisar ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS), da Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojan ƙasa, sai Rear Admiral Idi Abbas hafsan sojan ruwa, da kuma Air Marshall Kennedy Aneke a matsayin hafsan sojan sama.

A yayin tantance su, shugabannin sojan sun amsa wasu tambayoyi daga ƴan majalisar bayan gabatar da kansu da tarihin ayyukan da suka gudanar kafin naɗin nasu.

A cewar Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, tabbatar da su a matsayin jagororin ya sabunta zimmar gwamnatin Shugaba Tinubu akan sauye-sauye a fannin tsaro da mayar da hankali wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Babaji