Badaƙalar N400bn: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci a sake gurfanar da El-Rufa’i bayan soke hukuncin farko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kaduna, ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a shari’ar kare haƙƙin ɗan-adam da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar.

A hukuncin da alƙalai uku suka yanke a ranar 17 ga Maris, kotun ta ce an gudanar da shari’ar a matakin farko ne ba tare da cikakken adalci ba, wanda ya saɓa wa haƙƙinsa na samun sauraro na adalci, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kwamitin alƙalan da suka yanke hukuncin ya haɗa da Onyekachi Otisi, Abimbola Obaseki-Adejumo, da Sybil Gbagi.

Akan haka ne kotun ta soke dukkanin hukuncin shari’ar da aka yi a baya, tare da umartar a sake sauraron ƙarar a gaban wani sabon alkali.

Shari’ar ta samo asali ne daga binciken da kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta gudanar wasu maƙudan kuɗaɗe, bashin gwamnati da kwangiloli da aka gudanar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Kwamitin na zargin El-Rufai ne da hannun a badaƙalar jimillar Naira biliyan 400 a lokacin da yake gwamnan Kaduna.

By Babaji