Guardiola ya caccaki CAF kan ƙwace AFCON a hannun Senegal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana mamaki game da hukuncin Hukumar kula da Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) na ƙwace Kofin ƙasashen Nahiyar Afirka AFCON na 2025 da bai wa ƙasar Moroko, yana mai cewa an ɗauki matakin ne ba tare da adalci ba.

Ya bayyana cewa, wannan matakin abu ne da aka ɗauka ta bayan fage, inda ya ce ya yi mamaki matuƙa a kai.

Kwanaki biyu da suka gabata ne CAF ta sanar da ƙwace nasarar AFCON na 2025 daga hannun Senegal da bai wa Moroko bayan ƙorafi da hukumar ƙwallon ƙafa ta Moroko ta yi akan nasarar gasar.

Kalaman Guardiola na zuwa a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa akan tsare adalci yayin ɗaukar mataki a harkar ƙwallon ƙafa musamman akan manyan gasa irin su AFCON.

A wani ɓangare, kocin ya bayyana cewa mai tsaron gida na biyu a Manchester City, James Trafford ne zai tsare raga a wasan ƙarshe na kofin Carabao da za ta kara da Arsenala gobe Lahadi.

By Babaji