Ballon d’Or: Akwai yiwuwar Lamine Yamal ya lashe babbar kyauta da Kopa Trophy

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masu shirya taron karrama ‘yan wasa na Ballon d’Or da aka saba gudanarwa a kowace shekara sun tabbatar da cewa ɗan wasa zai iya lashe sama da kyauta ɗaya a taron a lokaci guda, a wani yunƙuri na bayar da amsa akan tambayoyin jama’a kan taron mai tsawon tarihin shekaru 70 da farawa.

A cewar jaridar Daily Post Nigeria, hanyoyin zaɓe da bayar da sunan ɗan wasa suna cin gashin kansu ne. Babu wata doka da ta haramta wa ɗan wasa samun kyauta sama da guda yayin taron na “the gala”. Wannan warwara na da alaƙa da ‘yan wasa huɗu gabanin taron na 26 ga Oktoba.

A ɓangaren maza, Lamine Yamal da Pau Cubarsi sune ake sa ran su lashe sama da kyauta ɗaya bayan shiga sahun ‘yan Ballon d’Or da Kopa Trophy, wanda ke karrama mafi hazaƙar ɗan wasa cikin masu tasowa.

TNT Sports ta ce Yamal mai shekaru 19 ya shiga sahun ‘yan wasan ne a mataki mai ƙarfi tare da ɗan wasan gaba na Ingila, Harry Kane.

A ɓangaren mata kuwa, mai tsaron gida ta ƙasar Sifaniya, Cata Coll da golar Brazil, Lorena sune waɗanda ka iya lashe kyautar Ballon d’Or ta mata da gwarzuwar mai tsaron gida ta shekara.

Saboda ba a taɓa samun wanda ya lashe kyauta biyu ba a lokaci guda a tarihin taron, dukkan ɗan wasan da ya samu biyu a bana, zai kafa sabon tarihi.

By Babaji

Leave a Reply