Ban ɗau fiye da mintuna uku ba kacal, inji mai fyaɗe

Wani mai fyaɗe, Sangokunle Akintola, wanda ya raka abokinsa Ismaila Raimi, domin koya wa wata budurwa darasin da ba za ta taɓa mantawa ba, ya shaida wa ’yan sandan jihar Osun cewa, bai wuce mintuna uku ba a lokacin da ya ke yi wa budurwar fyaɗe.

Ismaila ya kasance yana abota da yarinyar tsawon wata shida, yana ba ta kuɗi masu yawa kuma yana fatan ya aure ta a gaba.

Sai dai da yarinyar ta ce masa bai dace da damfara ba ‘Yahoo’, sai ya sha tabar wiwi, ya ɗauki sanda ya yi amfani da shi a matsayin bindiga ya nufi gidan su yarinyar.

Daga zuwa su gidan budurwar suka tarar da wani saurayi, inda suka tsoratar da shi da bindigo, suka fitar da ita waje suka yi fara yi ma ta fyaɗe.

Bayan kama su, Akintola ya shaida wa jami’an ’yan sanda cewa bai ɗau tsawon mintuna uku a kanta ba.

Mai fayɗen ya ce, “ban san me za mu je gidan budurwar mu yi ba. Ismaila kawai ya ce in raka shi wurinta ne. Mun isa wurin da misalin ƙarfe 7:30 na dare. A Kajola-Ile, Osogbo, sai muka haɗu da wani saurayi inda muka yi amfani da bindigar bogi don tsorata shi, sai muka kai yarinyar bayan gida muka yi lalata da ita. Ismaila ya fara yi ma ta fyaɗe a lokacin. Na ce masa ni ma zan so in yi nawa. Ba ma kai mintuna uku ba.”