An gano wanda ya sace Naira Miliyan 88.1 bayan shekaru 52

Theodore John Conrad, wani mutum mai shekaru 20 a watan Yulin 1969, a lokacin ya fara aiki a wani banki da ke Amurka. Bayan fara aikin ne ya sace Dala 215,000, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 88,182,250 a kuɗin Nijeriya, daga nan babu wanda ya sake ganin sa.

CNN ta ruwaito yadda darajar kuɗin da ya sata a yanzu ta kai $1.7m (N697,255,000) wanda shi ne mafi girman sata da aka taɓa yi wa banki a tarihin duniya.

Ya koma wani garin fiye da shekaru 50 da suka shuɗe daga baya ’yan sanda su ka bayyana cewa ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba sun gano shi.

Bayan fashin da ya yi wa bankin, Conrad ya koma wani garin, Boston kuma ya mayar da sunansa Thoman Randele.

Kamar dai yadda muke gani a fim, wani abu da zai ba ka mamaki shi ne, gidan mutumin kusa da inda aka shirya fim ɗin nan da ya shahara ‘The Thomas Crown Affair’. A fim ɗin jarumin ya saci $2,000,000 (N820,300,000) daga wani banki.

Dama Conrad ya saci kuɗin ne a ranar Juma’a bayan an rufe bankin, kuma ba a farga da satar ba sai ranar Litinin da aka lura bai zo aiki ba. Duk da yadda hotunan mutumin su ka dinga yawo, babu wanda ya samu nasarar jin wani labari akansa.

Ya ci gaba da rayuwarsa sai a watan Mayun 2021 yana da shekaru 71 ya rasu sakamakon cutar dajin huhu.