Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya ya sauka a Aswan na ƙasar Masar, inda ya koro wasu irin nau’ukan kunamai masu haɗari zuwa neman mafaka a gidajen mutane.
Mutane 3 ne AlJazeera ta ruwaito suka mutu inda sama da 400 ke kwance a asibiti a faɗin jihar domin karɓar maganin dafin kunama, a cewar kafafen yaɗa labarai na gwamnati.
Sai dai kuma muƙaddashin ministan lafiya na ƙasar, Khalid Abdel-Ghafar, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, ba a samu rahoton mace-mace ko ɗaya ba.
Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta tabbatar wa da jama’a cewa, tana da isassun adadin maganin dafin, inda ta ce an samu allurai 3,350 a Aswan.
Mamakon ambaliyar ruwan ya kuma tilastawa hukumomin yankin dakatar da makarantu a ranar Lahadin da ta gabata, inji gwamna Ashraf Atia.
Mutanen da kunamai suka harba sun ce alamomin da suke ji sun haɗa da zafi mai tsanani, zazzaɓi, gumi, amai, gudawa, ciwon jiki, da juyawar kai.
Da ma dai can tsaunukan Aswan yanki ne mai yawan kunaman Larabawa masu faɗin wutsiya waɗanda aka fi sani da ‘Androctonus crassicauda’, wanda ke nufin ‘mai kisan mutum’ a yaren Girkanci. Ana la’akari da su a cikin kunamai mafi haɗari a duniya, tare da dafin da zai iya kashe mutum a cikin sa’a guda bayan harbi. Abu ne sananne cewa, harbinsu yana haddasa mutuwar mutane da dama a shekara.
Nau’in kunaman na da tsayin inci 3 zuwa 4, kuma su na dogara ne da jijjiga da sauti, don gano abin da suke hari kasancewar ba sa gani, ji ko jin ƙamshi.
Hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna cunkoson tituna da lalatattun gidaje da ababen hawa da gonaki. Ruwan saman ya kuma haifar da ɗaukewar wutar lantarki.