Marigayi Yusuf Maitama Sule bai saci Kwabon al’umma ba – Jega

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfasa Attahiru Jega, ya shaida cewa, Marigayi Ɗanmasanin Kano, AlhajiYusuf Maitama Sule bai yi almubazaranci ko satar kuɗaɗen jama’a ba a lokacin rayuwar sa da ya riƙe muƙaman gwamnati daba-daban, tun yana ƙuruciyar sa.

Fitaccen malamin jami’a Jega, ya yi wannan furuci ne yayin gudanar da wata lakca kan shugabanci domin girmama Marigayi Ɗanmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule wadda gamayyar ɗaliban arewacin ƙasar nan ta shirya, wanda aka gudanar a cibiyar Umaru Musa Yar’adua da ke Jami’ar Katsina a ranar Litinin da ta gabata.

Kamar yadda shehin malami Jega ya ce, yayin da ake bayyana kyawawan halaye na Marigayi Ɗanmasanin Kano, wanda ya bayyana shi a matsayin uba a gare shi, wanda kuma ya yi masa riƙon mutunci, sai ya ce, “Marigayi Ɗanmasanin Kano, mutum ne da nake martaba wa kuma uba ne a gare ni a dukkan tsawon zaman ɗalibanci na a Kano, da zamana na malamin jami’a da kasancewa ta muƙaddashin shugaban jami’a, har ya zuwa rasuwar sa. Haƙiƙa ya kasance uba a gare ni.

“Marigayin ya bauta wa ƙasar nan da zuciya ɗaya cikin mutunci da yakana, a matsayinsa na minista tun yana ɗan yaro, lokacin da ya wakilci arewacin Nijeriya a majalisar ƙasa, lokacin da likkafar sa ta cira ya riƙe kujeru uku daban-daban na minista da suka haɗa da ministan makamashi, tama da ƙarafa, da kuma na man fetur, kuma a dukkan waɗannan ayyuka bai saci kwabon jama’a ba.”

Farfesa Attahiru Jega sai ya jinjina wa gamayyar ɗaliban bisa hangen nesan su da kuma girmama Marigayi Ɗanmasanin Kano, tare da addu’ar Allah ya kyautata kwanciya.

Jega ya ce, “Ina son yaba wa gamayyar ɗaliban bisa hangen nesan su na girmama wanda ya cancanta a girmama, kuma bisa hangen su na ganin buƙatar jera tafiya da matasan arewacin ƙasar nan, matuƙar muna buƙatar tsamo kawunan mu daga tashin-tashina da suka wofantar da ƙasar nan.”

A dai wurin lakcar, ƙwararru sun yi jawabai masu riƙe zuciya akan taken sa na,’Illolin Siyasa, Walwala Da Tattalin Arziki Kan Yawaitar Ƙofofin Shige Da Fice A Arewacin Nijeriya.’

Ya ce yayin da Nijeriya take da keɓaɓɓun hanyoyin shiga da fice guda 84 da suke da kyakkyawan tsaro, ƙasar tana da haramtattun ƙofofin shige da fice kimanin guda 1,499 da aka tantance a shekara ta 2003.

Tsohon shugaban hukumar zaɓen ya bayyana cewar, ga waɗannan haramtattun ƙofofi ne mutane suke tayin karakainar shige da fice wa ƙasar nan ɗauke da abubuwa da suke da nakasu akan walwalar tattalin arziki da ci gaban siyasar ƙasar nan.

Ya gane da cewar, akwai ƙanana da manyan makamai daga cikin manya-manyan haramtattun abubuwa da ake shigowa da su cikin ƙasar Nijeriya ta waɗannan haramtattun ƙofofin shige da fice.

Daga nan sai Jega ya yi kira ga shugabannin arewacin ƙasar nan bisa buƙatar su samar wa lardin kyakkywan shugabanci na rashin son zuciya.

Jega ya nuna takaicin sa bisa munanan ƙididdiga na ban tsoro da suka jiɓanci talauci, rashin ayyukan yi da rashin tsaro da suka yi wa arewacin ƙasar nan katutu, waɗanda ya danganta su da rashin kyakkyawan shugabanci, son zuciya, rashin hangen nesa da dabarbaru na shugabanni.

“Walau dai ƙalubalolin talauci, rashin ayyukan yi, rashin tsaro, mutuwar ƙananan yara, rashin halartar ‘ya’ya makaranta, rashin ilimin ‘ya’ya mata, aurar da ƙananan ‘ya’ya mata, da duk abinda zuciya kan tuna, dukkan su sun ta’allaƙa ne kacokan a arewacin ƙasar nan,” inji Jega.

Ya bayyana Marigayi Maitama Sule, tsohon wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin mutum maras son zuciya, mai tsananin kishin ƙasa, wanda ya bauta wa ƙasar nan iyakar-iyawar sa, haɗi da kare al’ummar arewa. Ya rasu yana da shekaru 88, a watan Yuli na shekarar 2017.

Jega sai ya kira yi matasa da su balagantar da kawunan su ta hanyar taka rawa a cikin siyasar ƙasar da zummar hana ‘yan iska daga lalata tattalin arzikin ƙasar nan.