Ban san inda na caka wa Ummita wuƙa ba, cewar ɗan Chana

Spread the love

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

A cigaba da zaman sauraron shari’ar ɗan asalin ƙasar Sin ɗin nan, Mista Frank Geng, da ake zargin ya kashe budurwarsa mai suna Umulkhulsum Sani Buhari dake zaune a Unguwar Janbulo cikin birnin Kano tun kimanin watannin baya, Mista Geng ya faɗa wa kotu cewa, bai san inda ya caka wa Ummita wuƙa ba.

A zaman na jiya Alhamis, 12 da Laraba 11 ga Janairu, 2023, da ya gudana a babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, Frank ya ce, ya kashe wa Ummita sama da Naira miliyan sittin daga haɗuwarsu a wata Yuni zuwa lokacin da abin ya faru.

Ya gabatar da shaida, lauyan wanda ake zargin, Barista Muhammad Balarabe Dan’Azumi, Mista Frank ya tabbatar wa kotun cewa, shi Musulmi ne, kuma ɗan kasuwar ƙasa da ƙasa da yake aiki da kamfanin BBY Textile dake kasuwar Kantin Kwari a matsayin kwansaltan.

Haka kuma ya qara da cewa, a watan Yuni na shekarar 2020 ita Ummita ta samu lambar wayarsa daga wajen ƙawarta ta kira shi inda ta bayyana masa ƙudurinta na son tarayya da shi kuma in Sha Allahu za ta aure shi.

“Ya ce mun fara soyayya a wata Yuli da ita inda ta fara tambayata kuɗi da nan take na yi mata dukkan abin da take buƙata saboda son da nake mata, kuma ban san in bata mata rai.”

Ya kuma bayyana cewa a watan Fabrairu, 2022 Ummita ta auri wani a Abuja da ba shi ba, inda ya samu karayar zuciya.

Haka zalika ya ce Ummita ta sanar da shi cewa ta rabu da mijinta, inda ta buƙaci ya dawo don ci gaba da soyayya tare da ita, inda ta ƙara alƙawarin aure da shi karo na biyu.

Mista Geng ya ce duk lokacin da ya je gidansu Ummita don ɗaukarta zuwa cin abincin rana mamarta tana farin ciki, tare da tura mata kuɗi a asusun bankin ta na GT bank.
 A rana ta biyu kuma jiya Alhamis a zaman kotun ya ciga ba da cewa ta ci gaba da tura masa bidiyo da hotunan sabon saurayinta ta WhatsApp, inda ya ce babu daɗi kuma cin mutunci ne don tana gaya masa wannan mutumin shi za ta aura.

Frank ya ce bayan nan kuma Ummita ta fara kiransa da ɗan uwanta kuma direbanta kuma idan ya kira ta ba ta ɗaga wayarsa tare da ƙin mayar masa da amsa.

Daga baya Ummita ta buƙaci ya tura mata karenta da yake hannunsa, sannan ta ƙi ta fahimce shi.

Bayan wannan kuma ya ce ya ɗauki karen zuwa gidansu ya isa ƙofar gidan ya kira wayar amma ta ƙi ɗauka sai ya ƙara kiran ƙanwarta mai suna Asiya ita ma ta ƙi ɗauka, yana tsaye har tsawon lokaci. 

Daga baya wani maƙwabcin su mai suna Mustapha ya fito ya gansa nan take ya kira qanwar Asiya amma ba ta ɗaga ba daga bisani suka buɗe ƙofar tare da kora karen wanda suka turo Mr Frank waje tare da rufe ƙofar gidan.

Daga bisani buɗe ƙofar tare da barinsa shiga amma kuma ya ce Ummita ta ci gaba da zaginsa tare da marinsa gaban mahaifiyarta da ƙanwarta Asiya, bayan ta fito daga ɗakin baccinta cikin fushi ta ƙoƙarta rufe ƙofa tare da kama shi da faɗa wanda ta koma ɗaki da ɗauko wuqa ta dawo inda yake tsaye lokacin, ya ce ta nufo shi da wuƙar amma ya yi ƙoƙarin karɓe wuƙar nan, take ta cijesa a kafaɗa da ɗan yatsa tare da turo shi.

Ganin haka Ummita ta ce ma ƙanwarta ta kira ‘yan sanda da jami’an kula da iyokokin ƙasa wato magirashan su fita da shi daga nan.

Bayan haka ya ce Ummita ta yi ƙoƙarin tura shi ɗakin baccinta tare ɗan kada ya gudu har sai jami’an tsaro sun zo sun tafi da shi, don ta ce ya yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe, kamar yadda ya shaida wa kotun a rana ta biyu.

Ganin abin da yake faruwa ne mahaifiyar Ummita ta tsawatar mata amma Frank ya ce ba ta ji maganar mamarta ba ta ci gaba da ƙoƙarin marinsa, wanda ya yi sanadiyyar faɗuwar gilashinsa dake a fuskarsa da ya jawo ganinsa ya ragu tare da gani garara-garara cikin ƙoƙarin ta na karɓe wuƙar marigayiya Ummita ta yi amfani da hannuwanta biyu wajen ƙoƙarin shaƙe shi kamar yadda ya ce, amma shi kuma wajen kare kansa ya yi amfani da wuqar dake gefensa ya caka mata a kafaɗa da ƙafarta.

Frank ya ce bayan faruwar hakan ne bai san haka ba sai bayan kwana biyu wani makwabcin su Ummita wanda ake kira Aminu ya je ya same shi tare da gaya masa fa ‘yan sanda  na nemansa tare da shaida masa abinda ya faru, sannan ya san haka, sai ya fara kuka a lokacin don bai yi niyyar kasheta ba, inji shi.

Daga nan lauyan wanda ake zargi da kisa Barista Muhammad Balarabe Dan’Azumi ya buƙaci a daga ƙarar don samun damar gudanar da binciken wasu shaidun da zai gabatar.

Nan take Alƙalin kotun Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage zaman zuwa ranar 7 da 8 ga Fabrairu, 2023 don cigaba da shari’ar.

By Editor