Bankin Duniya zai kashe dala miliyan 300 don taimakon ‘yan gudun hijira a arewacin Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan 300 domin gudanar da wasu ayyukan da ya ce zai inganta rayuwar ‘yangudun hijira a arewacin Nijeriya.

A wata sanarwa da jaridar Blueprint ta ruwaito, bankin ya ce a shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ‘yangudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.i

Bankin ya ce rikice-rikice da suka daɗe suna addabar oiiiii sun raba sama da mutum miliyan 3.5 da muhallinsu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.

“Daga cikin ƙangarorin da za mu mayar da hankali akwai irage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.”

“Muna matuƙar farin ƙaddamar da wannan aikin domin taimakon Nijeriya wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta,” inji Mathew Verghis, daraktan Bankin Duniya a Nijeriya.

By ukarofi